Gobarar ofishin INEC: Hotunan kayayyaki da takardun da ta lashe
- Wasu takardu da kayayyaki duk sun kone sakamakon gobara da ta tashi a hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ke Abuja
- Wannan ya biyo bayan matsalar wutar lantarki da aka samu a ofishin daraktan zabe da jam'iyyu da ke hedkwatar
- Kwamishin hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa, wanda ke da alhakin yada labarai da wayar da kan masu zabe, Festu Okoye, ya jaddada cewa lamarin bai tsananta ba
Wasu takardu da kayayyaki duk sun kone sakamakon gobara da ta tashi a hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ke Abuja.
Wannan ya biyo bayan matsalar wutar lantarki da aka samu a ofishin daraktan zabe da jam'iyyu da ke hedkwatar.
Jami'an hukumar kashe gobara ta babban birnin tarayya ne suka gaggauta isa ofishin don tsayar da gobarar tare da kasheta.
Kwamishin hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa, wanda ke da alhakin yada labarai da wayar da kan masu zabe, Festu Okoye, ya jaddada cewa lamarin bai tsananta ba.
Ya kara da cewa babu wata takarda mai matukar amfani da aka rasa a gobarar.
KU KARANTA: COVID-19: Titunan Kano bayan dokar hana zirga-zirga ta fara aiki (Hotuna)
A yau ne Legit.ng ta ruwaito cewa, labarin da muke samu da duminsa na nuna cewa hedkwatar hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC dake birnin tarayya Abuja na ci bal-bal yanzu haka.
The Nation ta ruwaito cewa gobarar ta fara ne lokacin Azahar kuma har yanzu tana zalzala.
Wannan shine karo na uku da manyan ofishohin gwamnatin tarayya a Abuja ke gobara duk da cewa babu maaikata a ofishohin.
An umurci maaikatan gwamnati suyi zamansu a gida saboda dokar ta bacin da gwamnatin tarayya ta sanya a Abuja.
A ranar Larabar nan, 14 ga watan Afrilu 2020, gobara ta tashi a hedikwatar hukumar yi wa kasuwanci rijista ta kasa (CAC) da ke unguwar Maitama a birnin tarayya, Abuja.
Gobarar ta babbake hawa na karshe a ginin ofishin hukumar CAC mai bene hawa bakwai, tare da lalata muhimman kayayyaki.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng