June Almeida: Matar da ta fara gano kwayar cutar corona a duniya

June Almeida: Matar da ta fara gano kwayar cutar corona a duniya

June Dalziel Ameida, ita ce matar da fara gano kwayar cutar corona a jikin dan Adam.

Ta kasance diya ga wani direban motar bas a kasar Scotland da ke yankin nahiyyar Turai.

Duk da karancin ilimi na zamani sakamakon daina zuwa makaranta da ta yi tun tuna da shekaru 16, June ta yi fice a fannin daukar hoton kwayoyin cutar virus.

Binciken da Mrs. Almeida ta gudanar shekaru aru-aru ya zama wani bangare mai muhimmanci a yayin wannan annobar ta yanzu kamar yadda sashen Hausa na BBC ya wallafa.

Sabuwar annobar cutar covid-19 wadda ta mamaye duniya a yanzu, wata kwayar cutar corona wato coronavirus ce ke haddasa ta.

Dakta Almeida ce ta fara gano kwayar cutar a shekarar 1964 a wani dakin gwajin cututtuka da ke asibitin St Thomas a birnin Landan.

June Almeida: Matar da ta fara gano kwayar cutar corona a duniya

June Almeida: Matar da ta fara gano kwayar cutar corona a duniya
Source: Getty Images

Tarihi ya tabbatar da an haifi kwararriyar a ranar 5 ga watan Oktoban 1930 a gidan mai lamba 10 da ke titin Duntroon a birnin Glasgow na kasar Birtaniya.

Mahaifinta shi ne Harry Leonard Hart da kuma maifiyarta, Jane Dalziel (née Steven).

Bayan haihuwarta an sa mata suna June Hart kuma ta taso a wani gidan haya daura da filin shakatawa na Alexander Park da ke Arewa maso Gabashin birnin Glasgow.

Bayan daina zuwanta makaranta, ta samu aiki a matsayin ma'aikaciyar gwajin kwayoyin cututtuka a asibitin Glasgow Royal.

Dakta Almeida ta koma aiki a asibitin St Bartholomew da ke birnin Landan. Daga nan kuma ta koma Landan da zama don ci gaba da aikinta.

A ranar 11 ta Dasumbar 1954, ta auri Enriques Rosalio (Henry) Almeida, wani mai zane dan asalin kasar Venezuela.

Sun haifi diya guda da shi mai sunan Joyce kana kuma su ka koma kasar Canada da zama. A nan ta ci gaba da aiki a cibiyar binciken cutar daji wato Kansa ta Ontario Cancer Institute.

Gabanin samun lambar girma ta kwarewa a kan aiki inda ta zamo Dakta a fannin ilimi, ta wallafa mujallar rapid laboratory viral diagnosis a shekarar 1979.

A cewar wani marubucin kiwon lafiya George Winter, babu shakka Dakta Almeida ta goge a fannin daukar hoton kwayoyin cuta.

Ta shige gaba wajen amfani da wani tsari wanda yake nuna yadda kwayoyin cutar suke ta hanyar amfani da sinadarin 'antibodie' masu kare garkuwar jiki.

Kwarewar Dakta Almeida ya sanya ta yi suna a Birtaniya kamar yadda Mista Winter ya bayar da shaida a wani shirin Drivetime a gidan rediyon BBC na Scotland

An ja ra'ayinta a shekarar 1964 da ta sake aiki a asibitin koyarwa na St Thomas a Landan, asibitin da Firai Minista Boris Johnson ya yi jinya bayan ya harbu da cutar korona.

Winter ya ce dawowarta ke da wuya, ta fara hada gwiwa da Dakta David Tyrrell, wanda ke gudanar da bincike a bangaren mura a Salisbury a gundumar Wiltshire.

KARANTA KUMA: Covid-19: Duk da dokar tilasta zaman gida, baƙi 2,500 sun fice daga Najeriya

Mista Winter ya ce Dakta Tyrrell na gudanar da bincike ne kan majinar wasu 'yan sa-kai kuma tawagarsa ta gano cewa mutane na iya daukar wasu kwayoyin cutar da ke da alaka da mura, amma ba dukansu ba.

KARANTA KUMA: Covid-19: Duk da dokar tilasta zaman gida, baƙi 2,500 sun fice daga Najeriya

Daya daga cikin kwayoyin cutar ita ce wadda aka fi sani da B814, kuma an samo ta a majinar dalibin wata makarantar kwana da ke Surrey a shekarar 1960.

Mista Winter ya ce a baya Dakta Almeida ta taba ganin kwayoyin zarra kamar wadannan a yayin da take bincike kan ciwon hanta a jikin beraye da kuma murar kaji.

Daga baya Dakta Almeida ta yi aiki a makarantar ci gaba da karatun Likita ta Landan inda aka ba ta lambar girma.

Hazikar ta bar duniya a ranar 1 ga watan Dasumba na shekarar 2007 bayan ta shafe shekaru 77 a doron kasa.

Ya zuwa yanzu shekaru 13 kenan da mutwarta, an tabbatar da mata da lambar girma wadda ta dace da ita, a matsayin ganuwar da masu binciken kan annobar coronavirus ta yanzu za su fahimta tare da dogaro a kanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel