Yanzu-yanzu: Uwargidar Sarkin Daura ta rasu

Yanzu-yanzu: Uwargidar Sarkin Daura ta rasu

Inna liLLahi wa inna ilaihi raji'un

Labarin da ke shigo mana na nuna cewa Allah ya yiwa, Hajiya Binta Umar Farouq, uwargidar mai martaba sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk, rasuwa ranar Juma'a, 17 ga Afrilu, 2020.

Hajiya Binta ta rasu ne a garin Daura tana mai shekaru 70 bayan rashin lafiyar da tayi fama dashi.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta samu rahoton ne daga Sarkin Labaran Daura, Malam Usman Ibrahim, a Katsina.

Ya ce Hajiya Binta ta rasu ne misalin karfe 8 na safiyar Juma'a a fadar sarkin Daura kuma an birneta bisa koyarwan addinin Musulunci.

Ibrahim Ya ce an gudanar da sallar Jana'iza karkashin jagorancin Limanin Daura, Malam Suleiman Salisu.

Maragayiyar ta rasu ta bar yara shida da jikoki da yawa.

Har yanzu akwai dokar ta baci a garin Daura saboda takaita yaduwar cutar Coronavirus da ta addabi duniya.

Allah ya jikanta da rahama, ya sa ta huta.

KU KARANTA Yanzu-yanzu: Ana gobara a Hedkwatar INEC dake Abuja

Yanzu-yanzu: Uwargidar Sarkin Daura ta rasu
Yanzu-yanzu: Uwargidar Sarkin Daura ta rasu
Asali: Facebook

Awani labarin daban, Shugaban kwamitin ko ta kwana dake yaki da yaduwar annobar cutar COVID-19 a jahar Kano, Farfesa Abdulrazak Habib ya kamu da cutar COVID-19, watau Coronavirus.

Farfesa Habib na daga cikin mutane 12 da hukumar kare yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, ta fitar da sakamakon gwajin da ta musu a ranar Laraba, 16 ga watan Afrilu, inji rahoton Vanguard.

Wata majiya ta tabbatar da lamarin, inda ta ce: “Da gaske ne, kuma abin takaici, Farfesa Habib ya kamu da COVID-19, a yanzu haka an kwantar da shi a cibiyar killacewa dake Kwanar Dawaki.”

Farfesa Habib kwararren likita ne da ya goge a kan sha’anin cututtuka masu yaduwa, kuma shi ne shugaba na biyu a kwamitin yaki da ta COVID-19 ta jahar Kano da Gwamna Ganduje ya kafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Coronavirus: Yan Nigeria sun yiwa Buhari martani kan umurnin ci gaba da zama a gida| Kalla a shafin Legit TV Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: