Zancen shan wutar lantarki ta kyauta a Najeriya farfaganda ce - TCN

Zancen shan wutar lantarki ta kyauta a Najeriya farfaganda ce - TCN

Labarin shirin samar da wutar lantarki ta kyauta ga 'yan Najeriya na watanni biyu ba komai bace illa farfagandar da ba za ta iya aiki ba, kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya ya sanar.

Kamfanin samar da wutar lantarki ta kasa (TCN) ya dora laifin a kan kamfanin rarrabe wutar lantarkin da ya fara sanarwa cewa gwamnatin tarayya za ta ba 'yan Najeriya wuta kyauta.

Kamfanonin rarrabe wutar lantarki sun bada sanarwar ne a karkashin kungiyar kamfanonin rarrabe wutar lantarki, jaridar The Punch ta ruwaito.

A yayin martani a kan wannan ci gaban a Abuja a ranar Alhamis, manajan daraktan TCN, Usman Mohammed, ya ce bai san daga inda wannan bayanin yake fitowa ba.

Kamar yadda yace, "Amma zan sanar da ku cewa babu wani abu makamancin wutar lantarki ta kyauta da gwamnatin tarayya za ta samar. Ba ita bace mamallakiyar wutar lantarkin."

Mohammed ya kara da bayanin cewa gwamnatin tarayya ta mallaki TCN ne kadai amma kamfanonin samarwa da rarrabe wutar lantarki na masu hannayen jari ne.

Zancen shan wutar lantarki ta kyauta a Najeriya farfaganda ce - TCN
Zancen shan wutar lantarki ta kyauta a Najeriya farfaganda ce - TCN
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An samu karin mutum 35 da suka kamu da coronavirus a Najeriya, jimmila 442

Ya ce, "A masana'antar wutar lantarki, TCN ce kadai ta gwamnatin tarayya amma duk sauran kamfanonin na masu hannayen jari ne. Ban san ta yadda wannan labarin ya samo asali ba."

Mohammed ya musanta cewa duk masu yada labaran nan kawai suna yada farfaganda ne ba labaran gaskiya ba. Kuma akwai yuwuwar hakan ba za ta yuwu ba.

Ya ce, "A gaskiya akwai mutanen da ke shirya farfaganda tare da tsarata wacce kuma ba gaskiya bace.

"A tunanina mun fi bukatar wuta daidaitacciya a kasar nan ba wai ta kyauta ba."

Amma kuma, a ranar Alhamis da ta gabata, 'yan majalisar wakilai sun hada kwamitin hadin guiwa a kan bada wutar lantarkin watanni biyu kyauta ga 'yan Najeriya.

Kakakin majalisar wakilan, Femi Gbajabiamila, wanda ya jagoranci taron a Abuja tare da kamfanonin, ya ce kwamitin hadin guiwar za su tsara yadda za a sauwakewa jama'ar kasar nan wutar lantarkin ta watanni biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel