Yadda rufe kasashe soboda Korona za ta shafi ibada a watan Ramadan

Yadda rufe kasashe soboda Korona za ta shafi ibada a watan Ramadan

A watan Ramadan ne aka saukar da Al-Qur'ani mai girma kuma shine watan da Musulmai ke kwashewa suna azumi.

A kalla ana daukar kwanaki 29 ko 30 ana kauracewa ci, sha da kuma saduwa da iyali daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana.

Ana karfafa guiwar masu azumi da su karanta Al-Qur'ani tare da yin salloli na musamman bayan buda baki, wadanda ake kira da Taraweeh.

Amma kuma sakamakon barkewar annobar Coronavirus a duniya, dukkan al'amuran addinai dole su dakata ballantana wadanda ake tara jama'a a wuri daya.

Tuni gwamnati ta haramta taron jama'a don gujewa barkewar annobar. An rufe masallatai tare da dakatar da sallolin jam'i.

Yadda rufe kasashe soboda Korona za ta shafo ibada a watan Ramadan

Yadda rufe kasashe soboda Korona za ta shafo ibada a watan Ramadan
Source: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Hotunan yadda dan kamfai na mata ya zama takunkumin rufe fuska a Kenya

Gwamnatoci sun haramta buda baki wanda za a tara taron jama'a.

Gwamnatin Najeriya da kungiyar malamai ta kasa ba a barsu a baya ba. Sun bukaci jama'a da su hakura da duk wani taron addini da zai tattara jama'a masu tarin yawa a wuri daya.

Kungiyar malamai ta kasa ta bukaci jama'a da su yi sallar Taraweeh a gidajen su tare da salloli biyar na rana.

Kasashen duniya da dama sun saka dokoki daban-daban don takaita yaduwar annobar.

Kasar Saudi Arabia da Jordan sun dakatar da sallar Taraweeh a masallatai.

Ma'aikatar al'amuran addini, Da'awah da kuma shiriya ta kasar Saudi ta ce kowa yayi sallar taraweeh a gida a watan Ramadan don za a rufe dukkan masallatan kasar har sai annobar ta kare.

Hakazalika, kasar Misra ba a barta a baya ba. Ta bayyana cewa masallatan kasar za su kasance a rufe har sai babu wani mai cutar a kasar.

Kasar Malaysia ta bayyana cewa babu taron buda baki a kasar kwata-kwata.

Gwamnatin kasar Malaysia ta ce ba za ta lamunci taron buda baki ba a watan Ramadan.

A UAE kuwa, duk masu bada sadakar kayan buda baki ko abinci za su kai ne har gida. Babu wani tanti ko taro da za a hada don rabon kayan.

Kasashen Canada da Indonesia ba a barsu a baya ba. "Don biyayya ga dokokin nisantar juna, babu wata liyafar da za a shirya a watan Ramadan. Dole ne a kiyaye dokokin nisantar juna don gujewa yaduwar cutar," Minista Fachrul Razi yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel