Jawabi mai ratsa zuciya da Buratai yayi wa dakarun Najeriya da ke Borno

Jawabi mai ratsa zuciya da Buratai yayi wa dakarun Najeriya da ke Borno

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Buratai, ya yi kira ga dakarun soji a kan su nuna sadaukantakarsu yayin yakar Boko Haram.

Wannan kiran ya biyo baya ne bayan kwanaki kadan da ya koma yankin Arewa maso gabas don jagorantar sojin.

A kalla shekaru 10 kenan da sojojin suka dauka suna yakar 'yan ta'addan da suka halaka dubbai tare da hana miliyoyin jama'a zama gidajensu.

A wani sako da ya tura ga dakarun, Buratai ya ce daga yanzu gaba za a ci don alhakin kawo karshen Boko Haram na kan rundunar.

"Kiranmu na kwararru ne, kira don bautawa kasarmu, kiran bada kariya ga kasarmu ta gado wacce a koda yaushe muke alfahari da ita," yace.

"Dole ne kuma muyi alfaharin kiranmu da ake da kwararru kuma masu kishin kasa. Don haka dole ne mu fita don batar da 'yan ta'adda. Dole ne mu yi hakan yanzu. Babu lokacin da yafi yanzu.

Jawabi mai ratsa zuciya da Buratai yayi wa dakarun Najeriya da ke Borno
Jawabi mai ratsa zuciya da Buratai yayi wa dakarun Najeriya da ke Borno
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke matar da tayi wa hadimarta tsarki da tozali da barkano

"A wannan abun da muka saka gaba, babu damar nuna rashin kwazo. Rundunar sojin Najeriya dama can ita mai mayar da hankali ce, kishin kasa kuma ladabtattu wadanda na san babu raggo ko daya a ciki.

"Rayukan dakarun da muka rasa ba zai taba zama a banza ba. Dole ne mu yi alfahari da hakan," cewar shugaban rundunar.

Buratai ya yi kira ga kwamandoji da su jagoranci dakarun da ke karkashinsu da gwarzantaka.

"Kwamandojina na kowanne mataki, dole ne mu rike wadanda ke kasanmu. Dole ne mu saka musu kwarin guiwa da kalamai tare da ayyuka.

"Don yin nasarar saka kwarin guiwa a zukatan wadanda ke kasan ku, dole ne kwamandoji su nuna rashin gazawarsu. Idan kuwa gajiya ta bayyana, za su cire duk wani gwarzantakar na kasa da su," yace.

Shugaban rundunar sojin ya ce yana da tabbacin cewa sojojinsa za su iya. Ya tunatar da su cewa su yi amfani da dabarunsu na yaki don kawo karshen Boko Haram na har abada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel