Tirkashi: 'Yan damfara sun yi kutse a layin wayar wani gwamnan PDP
- A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Enugu ta ce an yi kutse a wayar tafi da gidanka ta gwamna Ifeanyi Ugwuanyi
- Daga nan sai aka yi amfani da wayar wajen kiran manyan jami'an gwamnati, kamar yadda kwamishinan yada labarai na jihar ya sanar
- Gwamnatin jihar Enugu na sanar da jama'a cewa duk wani kira ko sako da zai shigar musu ta layin ba daga gwamnan yake ba
A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Enugu ta ce an yi kutse a wayar tafi da gidanka ta gwamna Ifeanyi Ugwuanyi.
Daga nan sai aka yi amfani da wayar wajen kiran manyan jami'an gwamnati, kamar yadda kwamishinan yada labarai na jihar, Chidi Aroh, ya bayyana a wasikar da ya aika wa jaridar Premium Times.
"Gwamnatin jihar Enugu ta gano cewa anyi kutse a layin MTN na wayar mai girma gwamnan jihar Enugu.
"Yan damfarar sun yi amfani da damar wajen kiran manyan jami'an gwamnati.
"Gwamnatin jihar Enugu na amfani da wannan damar wajen sanar da jama'a aukuwar wannan lamarin tare da kira garesu da suyi watsi da duk wani kira ko sako da ya fito daga layin wayar.
KU KARANTA: COVID-19: An damke mutum 2 da ake zargi da yunkurin yada cutar coronavirus
"Jami'an tsaro tare da ma'aikatan kamfanin sadarwar sun san da kutsen kuma ana kan bincike don gano wadanda suka aikata hakan.
"Muna matukar bada hakuri a kan tozarci ko kuma takurar da 'yan damfarar za su iya kawowa ga jama'a," kwamishinan ya rubuta.
A wani labari na daban,rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta damke wata tsohuwa mai shekaru 75 wacce ake zargi da duka tare da zuba barkono a ido da gaban mai aikinta.
Makwabtan matar mai suna Comfort Obi ne suka mika ta gaban ofishin 'yan sanda da ke Ekumenyi a Abakaliki sakamakon tsananin zaluntar mai aikinta da take yi.
Ta farfasawa mai aikin jiki sakamakon tsananin dukan da take mata. Mai aikin mai suna Chidinma ta ce, an dauko ta ne daga Ohaji Egbema da ke jihar Imo kusan watanni 12 da suka gabata.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng