A binciki abin da ya sabbaba gobara a sansanin yan gudun hijira dake Ngala – Buhari

A binciki abin da ya sabbaba gobara a sansanin yan gudun hijira dake Ngala – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ma’aikatar kula da musufi da walwalar yan gudun hijira da ta gudanar da cikakken bincike game da sababin tashin gobara a Ngala.

Wani mummunan gobara ya tashi a sansanin yan gudun hijirar ne dake jahar Borno wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 14, tare da jikkata wasu da dama, inji rahoton Daily Trust.

KU KARANTA: Coronavirus: WHO ta nemi kasashen duniya su cika sharudda 7 kafin su janye takunkumi

Wannan ne tasa Buhari ta hannun kaakakinsa, Malam Garba Shehu ya nemi ma’aikatar ta binciko makasudin tashin gobarar tare da hanyoyin kauce ma sake aukuwar hakan a gaba.

Shugaban ya bayyana gobarar a matsayin wani lamari mai tayar da hankali, kuma abin tsoro, don haka ya bada umarnin a kai ma mutanen da lamarin ya shafa daukin gaggawa.

A binciki abin da ya sabbaba gobara a sansanin yan gudun hijira dake Ngala – Buhari

A binciki abin da ya sabbaba gobara a sansanin yan gudun hijira dake Ngala – Buhari
Source: Twitter

Sa’annan shugaban ya yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka mutu, tare da fatan samun saukin wadanda gobarar ta yi sanadiyyar jikkatarsu.

Wannan gobara dai ta fara ne da misalin karfe 2:15 na ranar Alhamis, kuma ta kona dakunan yan gudun hijira guda 1,250, yayin da 7 suka samu munanan rauni, 8 kuma da sauki sauki.

An dade ana samun gobara a sansanin yan gudun hijira, yan gudun hijira na cikin mawuyacin hali sakamakon fatattakarsu da yakin Boko Haram ya yi daga garuruwansu.

A wani labari kuma, Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya taya jama’an garin Chibok alhinin cika shekaru 6 tun bayan da mayakan Boko Haram suka sace yan matan.

Gwamnan ya tura wata tawaga mai karfi domin wakiltarsa wajen jajanta ma iyayen yan matan da yan uwansu, tare da taya su alhinin rashi, sa’annan kuma ya basu sako su kai musu.

Tawagar ta hada da kwamishinan, ilimi, harkokin mata, rage talauci da mai wakiltar Chibok a majalisar dokokin jahar Borno, kuma sun isar da sakon gwamnan ya iyayen yan matan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel