COVID-19: Za a rufe Masallacin Kudus a watan Ramadan

COVID-19: Za a rufe Masallacin Kudus a watan Ramadan

- Kungiyar malamai ta Jerusalem masu kula da masallacin Al-Aqsa ta bayyana cewa za a rufe dukkan masallacin a watan Ramadan

- Za a ci gaba da kiran sallah sau biyar amma ana shawartar jama'a da su zauna a gida su yi sallolinsu

- Kasar Jerusalem dai ta kasance kasar da ta kunshi wuraren bautar addinan Juda, Kiristanci da Musulunci amma duk an rufe su saboda annobar Coronavirus

Za a rufe masallacin Al-Aqsa (Kudus) da ke birnin Jerusalem har a kammala azumin watan Ramadan saboda barkewar annobar Coronavirus.

Malaman addinin musulunci ne suka sanar da rufe masallacin mafi daraja na ukun a fadin duniya.

Kungiyar kula da manyan masallatai ta kwatanta lamarin da abun alhinin. A wata takarda da ta fita a ranar Alhamis, kungiyar kula da manyan masallatan ta ce an sanar da rufe masallacin ne don biyayya ga fatawoyin malamai da shawarwarin masana kiwon lafiya na duniya.

Ana shawartar musulmai a kan su yi ibadun su a gidajen su cikin watan Ramadan don tabbatar da tsaron lafiya, in ji kungiyar.

Ramadan: An rufe masallacin Al-Aqsa saboda coronavirus
Ramadan: An rufe masallacin Al-Aqsa saboda coronavirus
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Masari ya dakatar da sallar Tarawihi da Juma'a, ya kuma sake rufe wata karamar hukuma

Amma kuma, za a ci gaba da kiran sallah har a cikin watan Ramadan din sau biyar a rana. Za a bar hadiman addini su shiga masallacin, takardar ta kara da cewa.

Kamar yadda aka saba, dubban Musulmi ne ke zuwa masallacin don sallar Taraweehi a watan Ramadan.

Musulmai sun yadda cewa daga nan ne aka dauka Annabi Muhammad SAW zuwa sama.

Kasar Jerusalem na da wuraren bauta masu matukar muhimmanci ga mabiya addinin Juda, Kiristanci da kuma Musulunci. Dukkan kuwa addinan sun dauka matakan hana yaduwar annobar.

A makon da ya gabata kamar yadda Al-jazeera ta ruwaito, an bukaci yahudawa da su zauna a gida don shagulgulansu tare da iyalansu kadai.

A wata babbar coci ta Sepulcher, an saba taruwa don murnan bikin Easter amma a ranar Easter da ta gabata, mutane kalilan ne suka samu halartar wurin sanye da takunkumin fuska.

A kalla mutane 140 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar a kasar Isra'ila sannan mutane 12,600 ne suka kamu da cutar.

Hukumomi a Falasdin sun bayyana mutuwar mutane biyu tare da mutane 400 da suka kamu da cutar a yankin yammaci da kuma Gaza.

Tun a ranar 25 ga watan Maris aka rufe dukkan Masallatai a Gaza.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel