COVID-19: Masari ya dakatar da sallar Tarawihi da Juma'a, ya kuma sake rufe wata karamar hukuma
Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya sanar da dakatar da yin sallar tarawihi da sallar Juma'a a cikin jam'i kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Gwamnan ya kuma datse shige da fice a karamar hukumar Dutsinma na jihar inda aka samu bullar coronavirus a jihar a ranar Laraba.
Hakan na zuwa ne mako guda bayan Masari ya rufe garin Daura inda mutum na farko da aka samu da cutar a jihar ya rasu.
A cikin sakonni da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, ya bayar da umurnin rufe dukkan manyan kasuwanni a jihar.
DUBA WANNAN: An kama wadanda aka killace saboda coronavirus suna zina da juna
Gwamnan ya rubuta cewa, "Kamar yadda muka yanke shawarar rufe duk wata karamar hukuma da aka samu bullar #COVID19, mun bada umurnun rufe karamar hukumar Dutsinma daga karfe 7 na safiyar gobe, 17 ga watan Afrilun 2020.
"Kazalika, mun bada umurnin rufe dukkan manyan kasuwanni daga gobe. An kuma dakatar da yin jamiin sallar Jumaa daga sati mai zuwa. Har wa yau, an dakatar da yin Tafsiri da sallar Tarawihi a dukkan masallatai.
"Mun kuma dakatar da bude gidajen wasa, kallon talabijin ko Sinima a jihar. An umurci jamian tsaro su tabbatar da cewa sun takaita shige da ficen mutane da kayayyaki a iyakokin jihar.
"Muna daukan wadannan matakan ne domin kare mutanen jihar mu, kasarmu da duniya baki daya. Muna kira ga mutane su yi biyaya ga dokokin domin ganin an dakile wannan annobar. #COVID19 gaskiya ne."
Mutum na farko mai dauke da coronavirus a Kano ya rasu ne a ranar 7 ga watan Afrilun 2020.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng