Akwai yiwuwar ayi aikin hajji a shekarar 2020 – NAHCON

Akwai yiwuwar ayi aikin hajji a shekarar 2020 – NAHCON

- Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta bayyana cewa akwai yuwuwar yin aikin hajji a wannan shekarar

- Shugaban hukumar, Alhaji Zikrullah Hassan ya ce alamu na nuna cewa kasar Saudi Arabia za ta iya shawo kan annobar daga nan zuwa watan Mayu

- Amma kuma akwai yuwuwar a samu karancin guraben da kasar za ta bada don gujewa cunkosun jama'a yayin aiwatar da aikin hajjin

Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta bayyana cewa akwai yuwuwar yin aikin hajji a wannan shekarar.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, shugaban hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya sanar da hakan ne a hirar da aka yi dashi a gidan rediyon tarayya na Najeriya.

Alhaji Hassan ya ce alamu da ke bayyana daga ma'aikatar lafiya ta kasar Saudi Arabia da kuma manyan ayyukan masarautar na nuna raguwar barkewar annobar Coronavirus.

Akwai yuwuwar cutar ta bace a watan Mayun 2020.

Akwai yiwuwar yin aikin hajji a shekarar 2020 – NAHCON
Akwai yiwuwar yin aikin hajji a shekarar 2020 – NAHCON
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: COVID-19: Hotunan yadda dan kamfai na mata ya zama takunkumin rufe fuska a Kenya

Ya ce, hukumar na kyautata zaton cewa za a yi aikin hajji a wannan shekarar.

"Wannan ne dalilin da yasa NAHCON ba ta tsaya da shirye-shiryen aikin hajjin bana ba," yace.

Ya shawarci maniyyata da su fara biyan kudin aikin hajjin koda kadan-kadan ne don akwai yuwuwar a yi aikin hajjin amma a rage yawan mutane saboda annobar.

"Idan hakan ta faru, gurbin da suka bamu za mu bada shi ne ga wadanda suka fara biya," yace.

Ya yi kira ga Musulmai da ke da niyyar yin aikin hajjin da su yi addu'a tare da amfani da dukkan wasu matakan da suka dace.

Shugaban, ya kara da bayyana cewa duk da wannan abun da hukumar ke hange na yuwuwar yin aikin hajjin bana, ta dakatar da shirinta.

Ya tabbatar da cewa hukumar ba za ta samu wata asara ta kudi ba don duk wasu ayyukan da suka shafi aikin hajjin suna yin shi ne a shari'ance.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel