Yan bindiga sun halaka mutane 6 a Neja, mutane 600 sun tsere daga gidajensu

Yan bindiga sun halaka mutane 6 a Neja, mutane 600 sun tsere daga gidajensu

Akalla mutane 6 ne suka gamu da ajalinsu a hannun gungun miyagun yan bindiga a wasu kananan hukumomin jahar Neja guda biyu, da misalin karfe 10 zuwa 12 na ranar Laraba.

Daily Trust ta ruwaito yan bindigan sun kashe mutane 5 a karamar hukumar Shiroro yayin da wasu da dama suka jikkata a harin, a garin Madaki, karamar hukumar Rafi inda suka kashe 1.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Gwamna ya raba ma matasa barasa don maganin cutar Coronavirus

Yan bindigan da yawansu ya kai mutum 50 sun kutsa kai cikin kauyen Manta ne a kan babura suna harbin mai kan uwa da wabi, a dalilin haka fiye da mutane 600 suka tsere daga gidajensu.

Yan banga sun yi kokarin karawa da yan bindigan, amma sai suka ga wani jirgi mai saukan angulu yana biye dasu, don haka suka ranta ana kare don tsira da ransu.

Yan bindiga sun halaka mutane 6 a Neja, mutane 600 sun tsere daga gidajensu

Yan bindiga sun halaka mutane 6 a Neja, mutane 600 sun tsere daga gidajensu
Source: UGC

“Mun tsere ne bayan mun ga wani jirgi mai saukan angulu yana shawagi a sama, don haka muka yi tsoron kada su dauka mu ma yan bindigan ne su bude mana wuta.” Inji wani dan banga.

A yanzu haka yan gudun hijiran sun tare a makarantar Firamari ta Bosso dake cikin garin Minna.

Hare haren biyu sun gudana ne a tare, wanda hakan yasa Yansanda suka rasa wanda za su kai ma dauki. Wannan ne hari na biyu da ake kaiwa yankin cikin kwanaki hudu.

Harin farko an kai shi ne a ranar Lahadi, inda yan bindigan suka kashe mutane uku a Maukujeri, suka yi ma wata yarinya fyade, suka raunata wani Fasto tare da sace mutane 13.

A wani labarin kuma, Akalla mutane 17 ne suka mutu yayin da jirgin yakin Najeriya ya jefa bamabamai a kauyen Sakotoku dake karamar hukumar Dambo ta jahar Borno, bisa kuskure.

TheCable ta ruwaito mafi yawan wadanda suka mutu a wannan harin sune mata da ne da kuma kananan yara, wanda suke wasa da zaman shan iska a karkashin wata bishiyar mangwaro.

Majiyoyi sun bayyana dalilin jefa bamabaman shi ne an sanar da rundunar Sojan sam cewa yan Boko Haram na taruwa a kauyen a ranar Alhamis, don haka ta shirya musu luguden wuta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel