Daga karshe: An kama wadanda suka kashe ɗiyar shugaban Afenifere (Hoto)

Daga karshe: An kama wadanda suka kashe ɗiyar shugaban Afenifere (Hoto)

- Jami'an 'yan sanda sun cafke mutum 4 da ake zargi da kisan Funke Olakunrin

- Funke Olakunrin diyar shugaban Afenifere ce, Chief Reuben Fasoranti

- An kasheta ne a ranar 1 ga watan Yulin 2019 a kan titin Kajola da Ore na jihar Ondo

Jami'an 'yan sanda sun damke mutum 4 da ake zargi da kisan Funke Olakunrin, diyar shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere, Chief Reuben Fasoranti.

An kashe Olakunrin ne a tsakanin titin Kajola da Ore na jihar Ondo a ranar 1 ga watan Yulin 2019, jaridar The Nation ta ruwaito.

Sifeta janar din 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ne ya tura kwamishinan 'yan sandan jihar don zakulo makasan.

Daga karshe: An kama wadanda suka kashe ɗiyar shugaban Afenifere (Hotuna)

Daga karshe: An kama wadanda suka kashe ɗiyar shugaban Afenifere (Hotuna)
Source: Twitter

A ranar 13 ga watan Yulin 2019, kwamishinan 'yan sandan tare da runduna ta musamman ta tarayya mai yaki da fashi da makami ne suka fara bincike a kan kisan kan.

Ta hakan ne kuwa suka damko mutane hudu tare da mika su gaban hukuma don fuskantar hukunci.

DUBA WANNAN: Tsaro: Rundunar sojin Najeriya ta samu sabbin makaman zamani don yaki da Boko Haram

Bayan yan sanda sun shafe watanni suna bincike sun kama wasu miyagu da suka yi sanadin kama Auwal Abubakar.

Kama Abubakar kuma ya yi sanadin kama sauran mutane biyu a gungun miyagun da suka hada da Mohammed Shehu Usman da Lawal Mazaje a garin Benin ta jihar Edo.

Rundunar yan sandan ta ce duk da cewa ta kama mutum hudu yanzu ana cigaba da zurfafa bincike domin kamo sauran yan kungiyar ta fashi da makami da suka gudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel