Wata sabuwa: Gwamna ya raba ma matasa barasa don maganin cutar Coronavirus

Wata sabuwa: Gwamna ya raba ma matasa barasa don maganin cutar Coronavirus

Wata sabuwa inji yan caca, gwamnan jahar Nairobi, babban birnin kasar Kenya, Mike Mbuvi Sonko ya raba ma talakawa kwalaben giya a matsayin abin dake maganain cutar Coronavirus.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN da na AFP sun ruwaito koda yake gwamnan ya yi wannan ikirari, amma tuni kamfanin giyar da ya raba da gwamnatin Kenya suka karyata shi.

KU KARANTA: Lafiya uwar jiki: Dabarun karfafa garkuwan jiki don kare kai daga kamuwa da cutar Coronavirus

Gwamna Sonko ya raba kwalaben giyan ne tare da kayan abinci ga talakawa, inda aka hange shi yana sanya kwalaben giyan cikin kayan abincin da ya raba ma jama’a.

A cewarsa, manufar raba kayan abincin shi ne domin rage ma talakawa radadin mawuyacin halin da suke ciki a sanadiyyar bullar annobar Coronavirus mai toshe numfashin dan Adam.

“Muna hadawa da kwalaben giya ne a cikin kayan abincin da muke raba ma jama’an mu, bincike na cibiyar lafiya ta duniya, WHO, da sauran kungiyoyin kiwon lafiya ya nuna giya na taka muhimmin rawa wajen magance Coronavirus.” Inji shi.

Wata sabuwa: Gwamna ya raba ma matasa barasa domin yaki da cutar Coronavirus
Gwamna Sonko
Asali: Facebook

Sai dai kamfanin LVMH dake hada giyan ta musanta Gwamna Sonko, inda tace:

“Shan giyan mu ko wani iri ne baya maganin kamuwa da Coronavirus ko kuma ya yi maganinta, muna kira ga jama’a su wanke hannuwansu a akai akai don kare kansu daga cutar.”

Kaakakin gwamnatin kasar, Cyrus Oguna yace babu wani binciken kimiyya da ya nuna giya na maganin Coronavirus, don haka ya gargadi yan siyasa da su kauce ma neman suna da cutar.

Kasar Kenya na da mutane 225 da suka kamu da cutar, kuma tuni ta takaita zirga zirgan jama’a don rage yaduwar cutar, amma gwamnati da masu kudi na taimaka ma jama’a da abinci.

Ita dai cutar Coronavirus na bukatar matakan kandagarki ne a yanzu sakamakon ba ta da magani, sai dai kuma ana iya kara karfin garkuwan jiki domin yaki da cutar idan ta shiga jiki.

Kamar yadda yan Hausa ke fadi idan kana da kyau sai ka kara da wanka, ga wasu daga cikin hanyoyin karfafa garkuwan jiki domin ya yaki cututtuka yayin da suka shiga jikin dan Adam;

- Kauce ma shan taba da sauran kayan hayaki

- Cin abinci mai kayan ganye

- Motsa jiki a kai a kai

- Rage kiban da ya wuce hankali

- Samun isashshen barci

- Tabbatar da tsaftar jiki da gabbai

- Rage damuwa a rai

Sai dai karfin garkuwar jiki yana raguwa yayin da shekaru ke karuwa, don haka tsofaffi basu da garkuwan jiki mai karfi, don haka suke bukatar cin abinci masu sinadaran inganta garkuwan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel