Cutar Coronavirus ta sake kama mutane 2 a jahar Katsina
Har yanzu tsugunni bata kare ba sakamakon cigaba da yaduwar annobar Coronavirus da ake samu a Najeriya, inda a yanzu haka an kara samun mutane 2 dauke da cutar a jahar Katsina.
Hukumar kare yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, ce ta tabbatar da haka cikin sanarwar da ta saba fitarwa game da cutar inda ta tabbatar da samun karin mutane 2 daga Katsina.
KU KARANTA: Lafiya uwar jiki: Dabarun karfafa garkuwan jiki don kare kai daga kamuwa da cutar Coronavirus
Hukumar ta sanar da hakan ne bayan gudanar da gwaje gwaje a kan mutanen, wanda sakamakon gwajin ne ya tabbatar suna da dauke da kwayar cutar COVID-19.
Biyo bayan samun wannan kari, jahar Katsina na da jimillan mutane 7 kenan dake dauke da cutar, yayin da mutum daya ya mutu.

Asali: Facebook
Idan za’a tuna wani likita a garin Daura ne ya fara kamuwa da cutar, sa’annan wannan likita shi ya fara mutuwa daga cutar a jahar Katsina.
Bugu da kari sauran mutanen da aka samu masu dauke da cutar a bayansa sun fito ne daga cikin mutanen da suka yi mu’amala da shi kafin mutuwarsa.
A yanzu haka dai ana kulawa da mutanen dake dauke da cutar ne a wani wuri da aka ware domin killace su dake cikin babbar cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya dake Katsina.
Ita dai cutar Coronavirus na bukatar matakan kandagarki ne a yanzu sakamakon ba ta da magani, sai dai kuma ana iya kara karfin garkuwan jiki domin yaki da cutar idan ta shiga jiki.
Kamar yadda yan Hausa ke fadi idan kana da kyau sai ka kara da wanka, ga wasu daga cikin hanyoyin karfafa garkuwan jiki domin yaki da cututtuka yayin da suka shiga jikin dan Adam;
- Kauce ma shan taba da sauran kayan hayaki
- Cin abinci mai kayan ganye
- Motsa jiki a kai a kai
- Rage kiban da ya wuce hankali
- Samun isashshen barci
- Tabbatar da tsaftar jiki da gabbai
- Rage damuwa a rai
Sai dai karfin garkuwar jiki yana raguwa da karuwar shekaru don haka tsofaffi basu da garkuwa mai karfi, shi yasa ake bukatar su da cin abinci masu sinadaran inganta garkuwan.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng