Tsaro: Rundunar sojin Najeriya ta samu sabbin makaman zamani don yaki da Boko Haram

Tsaro: Rundunar sojin Najeriya ta samu sabbin makaman zamani don yaki da Boko Haram

- Rundunar sojin Najeriya ta zaburo don yakar 'yan ta'addan Boko Haram a yankin Arewa maso gabas din kasar nan

- Rundunar ta karo makaman yaki na zamani don yakar 'yan ta'addan

- An gano cewa, sabbin ababen hawan na yaki na daga cikin kashin farko na makaman da kasar nan ta siya a kasar China

Gwamnatin kasar China ta ce kashi na farko na ababen hawan yaki da rundunar sojin Najeriya ta siya a kasar sun iso Najeriya.

Kamar yadda jaridar Ukdefencejournal ta ruwaito, ababen hawan sun hada da tankokin yaki masu kirar VT-4 da wasu ababen hawan biyu masu tuka kansu.

Rundunar sojin ta yi wannan siyayyar gaggawar ne daga hannun gwamnatin kasar China din a matsayin sabon salo na tsananta yaki da ta'addanci a yankin arewacin Najeriya.

Laftanal Janar Lamidi Adeosun, shugaban tsari na rundunar sojin, ya ce wannan kwangilar an sa hannu a kanta tsakanin Najeriya da NORINCO tun a 2019.

Dakarun sojin da ake tsammanin za su yi amfani da ababen hawan na yaki, an horar dasu tuni a kasar China.

Gwamnatin kasar China ta kara da cewa, kasar Najeriya ce ta farko a yankin nahiyar Afrika da ta fara mallakar irin wadannan tankokin yakin na zamani.

Tsaro: Rundunar sojin Najeriya ta samu makaman zamani don yaki da Boko Haram

Tsaro: Rundunar sojin Najeriya ta samu makaman zamani don yaki da Boko Haram
Source: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Hotunan yadda dan kamfai na mata ya zama takunkumin rufe fuska a Kenya

A wani labari na daban, 'yan gudun hijira 14 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da 15 daga ciki suka samu raunika daban-daban.

Hakan ya faru ne sakamakon barkewar gobara a sansanin 'yan gudun hijarar da ke karamar hukumar Ngala ta jihar Borno.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, gobarar ta fara ne da karfe 2:15 na yammacin ranar Alhamis a sansanin. Kamar yadda wata majiya ta tabbatar, an yi kokari wajen kashe wutar da gaggawa.

"A halin yanzu, ranar 16 ga watan Afirilun 2020, gobara ta kama a sansanin 'yan dudun hijira da ke Ngala. Gobarar ta lashe gidaje 1250 amma ba a tabbatar ba," majiyar ta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel