Yadda mutum na farko ya shigar da cutar coronavirus jihar Kano - Likita

Yadda mutum na farko ya shigar da cutar coronavirus jihar Kano - Likita

Sakamakon gwajin wani likita wanda ya yi cudanya da mutum na farko wanda cutar coronavirus ta harba a jihar Kano ya tabbatar ba ya dauke da cutar.

Likitan mai suna James King, a ranar Alhamis kan shafinsa na Facebook, ya tona asirin yadda mutumin na farko wanda coronavirus ta harba ya yi sakacin shigar ta cutar jihar Kano.

Ba tare da bayyana sunan wanda ya kamu da cutar ba, King ya zayyana yadda mara lafiyar ya garzayo asibitinsu kuma aka gaggauta mika shi wurin da aka tanada domin killace wadanda ake zargi su na dauke da cutar.

A rahoton da jaridar The Punch ta ruwaito, Dr. King wanda mazauni ne a jihar Kano, ya bayyana irin rashin hadin kai da suka samu daga bangaren mai dauke da hatsabibiyar cutar ta covid-19.

Ya ce mutumin ya ki bayyana wuraren da ya shiga, bayan kuwa ya halarci taron jama'a da dama.

Kwayoyin cutar coronavirus

Kwayoyin cutar coronavirus
Source: UGC

A cewarsa, mutumin ya ziyarci asibitinsu a ranar 10 ga watan Afrilu, inda ya yi korafin zazzabi, rashin kwari a jika, bushewar baki, da kuma rashin kwadayin abinci.

Ya ce, "ba mu sani ba ashe mutumin ya fita kasar waje inda ya biyo mota daga Abuja gabanin dawowarsa jihar Kano. A yayin da ya kamo hanya daga Abuja, ya kuma yada zango a Kaduna gabanin dawowarsa Kanon a ranar 25 ga watan Maris, 2020."

"Ya boye mana duk wuraren da ya shiga gabanin zuwansa Kano. Ya kuma boye mana cewa alamomin cutar covid-19 sun bayyana a kansa na daukewar numfashi da tari. Ya kuma boye mana cewa ya ziyarci asibitoci da dama bayan dawowarsa Kano"

"Bugu da kari, ya kuma boye mana cewa ashe an tura da samfurin jininsa zuwa ga hukumar dakile yaduwar cututtuka NCDC domin gwajin lafiyarsa gabanin ya gabatar mana da kansa."

King ya cigaba da cewa, "Abin da kawai mutumin yayi ikirari shi ne rashin jin dadin jikinsa na 'yan kwanaki kadan, ba tare da bayar da shaidar yana fuskantar numfashi da kyar, masassara da kuma tari."

KARANTA KUMA: Covid-19: Gwamnati ta biya N200bn don bunkasa samun wutar lantarki a Najeriya

"Bayan mun kammala duba shi ba tare da ya bamu duk wancan bayanai ba, mun ba shi gado a daya daga cikin dakunan marasa lafiya da misalin karfe 7.30 na yammacin ranar Juma'a 10 ga watan Afrilu."

"Ya yi cudanya da likitoci biyu da kuma masu taya likita aiki guda uku da kuma wani ma'aikacin mu guda daya."

"Mun kuma gano cewa a yayin da yake fama da rashin lafiya gabanin gabatar mana da kansa, ya halarci sallolin Juma'a, da sauran taro na jama'a,"

"Bayan wayewar gari, mahukunta lafiya sun garzayo asibitin da umarnin da gwamna ya basu na rufe asibitin baki daya."

"Sun dauke mara lafiyan zuwa wurin da gwamnatin Kano ta tanada a wajen gari domin killace wadanda ake zargin sun kamu da cutar coronavirus."

"Haka kuma an killace mu a cikin asibitinmu tare da daukar samfurin jinin mu domin aiwatar da gwajin covid-19."

"Bayan shafe kwanaki, ba mu da damar ganin iyalai ko 'yan uwanmu. Amma daga karshe sakamakon gwajin mu ya fito a ranar Laraba, 15 ga Afrilun 2020, kuma babu wanda cutar ta harba."

"Sai dai ya zuwa yanzu ba a bari mun fito daga inda aka killace mu ba." inji Dakta King.

Ya zuwa yanzu adadin mutanen da suka kamu da cutar ya kai 21 a jihar, bayan da aka sanar da karin mutum 12 da suka harbu da cutar a daren Laraba.

A karon farko an samu mutumin da cutar corona ta hallaka a jihar Kano da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel