Yanzu-yanzu: An sallami masu Coronavirus 5; 2 a Kwara, 3 a Akwa Ibom

Yanzu-yanzu: An sallami masu Coronavirus 5; 2 a Kwara, 3 a Akwa Ibom

An samu karin mutane 5 masu cuta mai toshe numfashi watau Coronavirus da suka samu sauki da lafiya bayan kwashe kwanaki suna jinya a jihar Kwara da Akwa Ibom.

A jihar Kwara, gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana cewa an sallami mutane biyu a jiharsa bayan gwaji biyu daban-daban sun nuna cewa sun barranta daga cutar.

Ya kara da cewa an sallamesu tare da yan uwansu da aka killace saboda ana tsoron sun kamu da cutar amma basu kamu ba.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai ranar Alhamis a Ilori, babbar birnin jihar.

Yace "Ina farin cikin sanar muku da cewa zamu sallami mutane bakwai daga cibiyar killace maras lafiyarmu."

" Cikin akwai mutane biyu da suka fara kamuwa da cutar a jiharmu."

A jihar akwa Ibom kuwa, gwamnatin jihar ta yi farin cikin sanar da cewa an sallami mutane uku cikin biyar masu cutar Coronavirus a jihar.

Kwamishanan lafiyan jihar, Dr Dominic Ukpong, wanda yayi sanarwan ya ce an sallamesu ne bayan gwajin karshe da akayi musu ya nuna cewa sun warke.

Yace “Gaba daya mutane tara muke da shi a cibiyar killace maras lafiyarmu. Ukun da zamu sallama yau sun kwashi cutar ne daga mutane biyar na farko da suka harbu a jiharmu.“

“Yanzu Akwa Ibom nada masu cutar 3 kacal, biyu daga cikin wadanda suka kawo cutar jihar, daya kuma wanda hukumar NCDC ta sanar jiya.“

KU KARANTA An kama wadanda aka killace saboda coronavirus suna zina da juna

Yanzu-yanzu: An sallami masu Coronavirus 5; 2 a Kwara, 3 a Akwa Ibom
Yanzu-yanzu: An sallami masu Coronavirus 5; 2 a Kwara, 3 a Akwa Ibom
Asali: UGC

A wani labarin mai alaka, Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane 34 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Laraba, 15 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An samu karin mutane talatin da hudu (34) sun kamu da #COVID19; 28 sun warke, kuma 2 sun rigamu gidan gaskiya.“

18 a Lagos

2 a Katsina

12 a Kano

1 a Delta

1 a Neja

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel