COVID-19: Hanyoyi 4 da gwamnati za ta iya isar da tallafi ga talaka cikin sauki

COVID-19: Hanyoyi 4 da gwamnati za ta iya isar da tallafi ga talaka cikin sauki

Bullar annobar coronavirus a kasashen duniya ya janyo sauye-sauye da dama a rayuwar al'umma kama ga yadda ake mu'amala da juna da kuma gudanar da ayyuka.

Galibin kasashen duniya dai su kan saka dokar takaita zirga zirga ko kuma hana fita baki daya idan an samu bullar cutar a kasashen su tare da rufe iyakoki na kasa da jihohi.

Ita ma Najeriya kamar sauran takwarorinta a duniya ta saka dokar hana fita a wasu jihohi kamar Legas, Ogun da Abuja. Kana daga bisani wasu jihohin su ma sun saka dokokin hana fitar ko takaitawa.

Saka dokar hana fitar yana nufin mutane da dama musamman masu karamin karfi za su shiga mawuyacin hali domin wasu daga cikinsu sai sun fita sana'a sannan suke samun abin kai wa baki.

Wannan dalilin ne yasa gwamnatin tarayya, jihohi, kamfanoni masu zaman kansu, manyan yan kasuwa da sauran attajirai suka rika bayar da kudi ko tallafi domin taimakawa marasa karfi a kasar.

Wani batun da ke ta janyo cece–kuce shine tsarin da za a bi wurin rabon kayan tallafin ga alummar kasar, hakan yasa Legit.ng ta yi nazarin wasu hanyoyi da gwamnatin za ta iya amfani da su domin isar da kayan tallafin ga al'umma kamar haka

COVID-19: Hanyoyi 4 da gwamnati za ta iya isar da tallafi ga talaka cikin sauki

COVID-19: Hanyoyi 4 da gwamnati za ta iya isar da tallafi ga talaka cikin sauki
Source: Facebook

1. Amfani da ma'aikatan hukumar samar da wutan lantarki – Ma'aikatan hukumar lantarki sun san dukkan lunguna da sako na birane da kauyuka saboda su kan kai wa mutane takardan kudin wuta.

Sun kuma san unguwanni masu hannu da shuni da na talakawa saboda haka gwamnati ko masu hannu da shuni na iya amfani da su a basu motoci domin isar da tallafin ga wadanda ya dace a ba.

DUBA WANNAN: An kama wadanda aka killace saboda coronavirus suna zina da juna

2. Amfani da lambar BVN ko Lambar waya – Wani hanya da gwamnati ko kungiyoyin bayar da tallafi za su iya amfani da ita domin raba kayan tallafi ko kudi ga mutane shine ta hanyar amfani da lambar da ke nuna adadin asusun ajiyar banki da mutum ya mallaka.

Tare da hadin gwiwa da bankuna ana iya nazarin irin hadahadar kudi da mutum ya saba yi hakan zai iya banbanci masu hannu da shuni da kuma talakawa da mabukata.

Daga nan ana iya aike wa mutanen da ake niyyar ba tallafin kudi da za su cire daga bankuna su biya bukatunsu musamman a wannan lokaci na annoba.

Kazalika, kamfanonin sadarwa suna iya taimakawa gwamnati da kididdigan kudin da mutane ke saka wa a wayoyinsu don a gano mabukata. Kamfanonin kuma suna da adireshin mutanen.

3. Amfani da masu rike da sarautun gargajiya – Masu rike da sarautun gargajiya kaman hakimai, dagatai da sauransu sun saba cudanya da talakawa kuma sun san halin da mutanen su ke ciki.

Gwamnati ko kungiyoyin jin kai za su iya neman bayanai daga hannun masu rike da sarautun gargajiya domin gano ainihin mabukata sannan a damka musu kayan tallafin tare da wakilai don a raba wa mutane.

A kowanne unguwa ana iya zaban wurin da ya dace a ajiye kayan a rika kirawo wadanda ake bukatar bawa kayayyakin cikin hikima ba tare da cinkoso ba.

4. Malaman addini da Limamai – Gwamnati tana iya tuntubar malama addini da limamai ko fastoci domin su ma suna da kusanci da talakawa kuma sun san gidajensu.

Malaman suna iya bayar da sunayen mutanen da su ke ganin suna bukatar irin wannan talafin ita kuma gwamnati a bangaren ta sai ta tura wakilai da za su saka ido kan yadda lamarin zai kasance.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel