Covid-19: Gwamnati ta biya N200bn don bunkasa samun wutar lantarki a Najeriya

Covid-19: Gwamnati ta biya N200bn don bunkasa samun wutar lantarki a Najeriya

Gwamnatin tarayya ta bayar da sahalewarta a kan biyan N200bn domin bunkasa samuwar makamashi na iskar gas ga kamfanoni masu rarraba wutar lantarki.

Daily Trust ta ruwaito cewa, gwamnati ta malalo wannan makudan kudi domin bunkasa samun wutar lantarki a kasar yayin da annobar covid-19 ta yi sanadiyar tilastawa al'umma zaman gida.

Shugaban kamfanin man fetur na kasa NNPC, Mallam Mele Kyari, shi ne ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba.

Shugaban kamfanin NNPC; Mele Kyari
Shugaban kamfanin NNPC; Mele Kyari
Asali: UGC

Shaidar Mallam Kyari ta zo ne bayan ganawarsa da ministan lantarki, Engr. Saleh Mamman da kuma shugaban kamfanin raba wutar lantarki na kasa, Usman Muhammad, a birnin Abuja.

Ya ce gwamnati ta biya fiye da Naira biliyan 200 cikin kwanaki biyu zuwa uku domin tabbatar da an samu wadatacciyar wutar lantarki a kasa baki daya.

Kyari ya ce an gudanar da zaman tattauna wannan lamari tare da ministan lantarki domin bunkasa samar da makamashin gas ga kamfanoni masu dakon wuta a kasar.

KARANTA KUMA: Covid-19: Nau'ikan abinci masu bunkasa garkuwar jiki

Ya sha alwashin kai ziyara wasu daga cikin kamfanonin rarraba wutar lantarki a yau Alhamis, domin tabbatar da 'yan Najeriya sun samu wuta a wannan lokaci da aka tilasta zaman gida.

A nasa jawaban, shugaban kamfanin dakon wutar lantarki reshen Neja Delta, Mr. Chiedu Ugbo, ya ce zai yi iyaka bakin kokarinsa wajen tabbatar da wannan muradi na gwamnati.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnati na ci gaba da daukan matakai na saukakawa al'ummar kasar nan daga matsi na rayuwa da cutar coronavirus ta jefa su a ciki.

A yanayin dai, a baya-bayan nan an yi rade-radin cewa, kamfanonin samar da hasken lantarki sun nemi hadin gwiwar gwamnati domin bayar da wutar lantarkin ta watanni biyu kyauta.

A na iya tuna cewa, gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, na daya daga cikin kusoshin kasar nan da cutar corona ta harba tun bayan bullarta makonnin da suka shude.

Ya zuwa yanzu gwamnan na Kaduna bai warke ba kamar yadda ya bayyana a Yammacin Laraba a kan shafinsa na zauren sada zumununta.

Sauran kusoshin da cutar ta harba su ne;

Abba Kyari - Shugaban Ma'aikata a fadar gwamnatin Najeriya,

Bala Muhammad - Gwamnan Bauchi,

Seyi Makinde - Gwamnan Oyo,

Muhammad Babandede - Shugaban hukumar kula da shige da fice

Sai dai tuni gwamnan na Bauchi da takwaransa na Oyo da kuma Babandede suka bayyana cewa sun samu waraka daga cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel