COVID-19: Ministan FCT ya sanar da kwanakin bude kasuwanni

COVID-19: Ministan FCT ya sanar da kwanakin bude kasuwanni

- Ministan babban birnin tarayya ya bayyana cewa za a fara bude kasuwannin a ranakun Laraba da Asabar

- Ministan, wanda ya sanar da hakan yayin taron kwamitin tsaro na yaki da annobar, ya jajanta yadda mazauna garin ke amfani da damar zuwa kasuwa don karya doka

- Birnin tarayyar zai shirya wayar da kai ga jama'ar karkara tare da hadin guiwar shugabannin kananan hukumomi, sarakunan gargajiya da kuma shugabannin al'umma

A kokarin ganin jama'a sun bi dokar hana zirga-zirga a babban birnin tarayya don hana yaduwar cutar coronavirus, ministan birnin tarayya ya bayyana cewa za a fara bude kasuwannin a ranakun Laraba da Asabar.

Ministan ya ce kotun tafi-da-gidanka za ta fara aiki don ladabtar da masu laifi.

Ministan, wanda ya sanar da hakan yayin taron kwamitin tsaro na yaki da annobar, ya jajanta yadda mazauna garin ke amfani da damar zuwa kasuwa don karya doka.

Ya ce mazauna garin basu bin dokar hana zirga-zirgar.

A wata takardar da sakataren yada labarai na ministan, Anthony Ogunleye ya fitar, ya ce an rage ranakun cin kasuwanni don haka kwanaki biyu kacal za su dinga budewa.

COVID-19: Ministan FCT ya sanar da kwanakin bude kasuwanni
COVID-19: Ministan FCT ya sanar da kwanakin bude kasuwanni
Asali: Facebook

KU KARANTA: COVID-19: FG ta bayyana gaskiyar lamari a kan lafiyar likitocin China da suka zo Najeriya

Ana shawartar mazauna yankin da su ziyarci kasuwannin kusa dasu don an haramta zirga-zirga daga yanki zuwa yanki.

"Kotun tafi-da-gidanka za ta fara aiki don hukunta dukkan masu laifi a fadin birnin tarayyar," yace.

Sabbin dokokin sun haramtawa babur yawo a Kubwa da Dutsen Alhaji yayin kullen.

Birnin tarayya zai shirya wayar da kai ga jama'ar karkara tare da hadin guiwar shugabannin kananan hukumomi, sarakunan gargajiya da kuma shugabannin al'umma.

Hakan zai sa su gane illolin muguwar cutar.

A wani labari na daban, mazauna garin Daura sun bayyana cewa kullen da suke fuskanta a garin ya kara musu yunwa ne don basu da kudin siyan abinci.

Kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa, Barista Ado Lalu mazaunin garin ne wanda yayi magana a madadin jama'ar garin.

"Da yawa daga cikinsu basu shirya wa kullen ba. Babu kudi balle mu siya kayan abinci mu ajiye. Da yawa daga cikinmu wadanda ke aikin kullum sun dogara da abokai da makwabta ne don ciyarwa," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel