COVID-19: Ana zargin mutane 170 na dauke da coronavirus a Sokoto
- Rundunar taimakon gaggawa ta jihar Sokoto a kan cutar coronavirus, ta ce mutane 170 ne ake kan bincika a jihar
- Shugaban kungiyar, Dr. Ali Inname ya sanar da wannan ne ga jaridar Daily Trust a wata tattaunawar waya da suka yi
- Kamar yadda yace, hakan zai sa su damko dukkan wadanda suka dawo din tare da killacesu don gwajin cutar
Rundunar taimakon gaggawa ta jihar Sokoto a kan cutar coronavirus, ta ce mutane 170 ne ake kan bincika a jihar.
Shugaban kungiyar, Dr. Ali Inname ya sanar da wannan ne ga jaridar Daily Trust a wata tattaunawar waya da suka yi.
Ya ce jihar za ta bi gida-gida ne don zakulo wadanda suka ziyarci Abuja ko Legas suka dawo garin.
Kamar yadda yace, hakan zai sa su damko dukkan wadanda suka dawo din tare da killacesu don gwajin cutar.
Ya ce wannan matakin zai shawo kan yaduwar ko barkewar annobar a jihar.
KU KARANTA: COVID-19: Lauyoyi sun yi gudun ceton rai bayan wanda ake zargi ya yi tari a kotu
A wani labari na daban, An samu wata kamar dirama a cikin wata kotun majistare dake jihar Osun.
Wani wanda ake zargi da cin zarafi ne ya yi tari yayin da ake karanto mishi laifukansa.
Wannan ci gaban kuwa ya kawo tangarda a shari'ar don kuwa lauyoyi uku ne suka gaggauta tserewa.
Duk da faruwar wannan lamarin kuwa, mai shari'a Olusegun Ayilara ya sanar da wanda ake zargin cewa tarinsa ba zai tsayar da abinda ake yi ba.
An gurfanar da Ige ne tare da wani mai suna Rasaq Sunday, Wasiu Adeyanju da Samson Ogunleye.
Ana zargin cewa a ranar 6 ga watan Afirilun 2020 a titin Olugun da ke Osogbo, sun hada kai wajen aikata laifi wanda ya ci karo da sashi na 516 na dokokin laifukan jihar Osun na 2002.
An zargesu da yin amfani da fasassun kwalabe, almakashi da adda wajen raunata wani mai suna Lateef Kareem.
Rasaq Olayiwola ne ya sanar da bayyanar masu gurfanarwar. Wanda ake zargin wanda bashi da lauya, ya musanta zargin da ake masa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng