Muna fuskantar kalubale a fagen yaki da cutar covid-19 a Najeriya - NCDC
Hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC, ta ce tana fuskantar manyan kalubale a fagen yaki da cutar covid-19 wadda ta zamto alakakai a sassan duniya daban-daban.
Shugaban hukumar Dr. Chikwe Ihekweazu, shi ne ya bayyana hakan da cewar yaga kwazo da nagartar ma'aikatar lafiyar kasar nan wajen lalubo wadanda ake zargi sun harbu da cutar corona.
Dr. Ihekweazu ya kuma bayar da shaidar yadda hukumar ke fuskantar kalubale wajen aiwatar da gwaji kan wadanda ake zargi domin tabbatar da sun harbu da cutar ko kuma sabanin haka.
Ya ce gwargwadon iko, a halin yanzu Najeriya tana da ikon aiwatar da gwajin kan mutane 1,500 a kowace rana.

Asali: UGC
Furucin Dr. Ihekweazu ya zo ne a ranar Talata, 14 ga Afrilun 2020, yayin ganawa da kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa kan cutar covid-19
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin jawaban da ya gabatar a ranar Litinin, ya bukaci hukumar NCDC ta kara himma wajen aiwatar da gwajin mutum 2000 a kowace rana.
KU KARANTA: Tunawa da harin Nyanya: Mutane sun koka da rashin kulawar gwamnati
A yayin da likafar cutar corona ke ci gaba a Najeriya, ya zuwa yanzu akwai fiye da mutane 400 da suka harbu da cutar a jihohi 19 da kuma babban birnin kasar.
Cikin rahoton da jaridar BBC Hausa ta ruwaito, a karon farko an samu mutumin da cutar corona ta hallaka a jihar Kano da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Ya zuwa yanzu dai adadin mutanen da suka harbu da kwayar cutar corona a jihar sun kai 21, yayin da ma'aikatar lafiya a jihar ta sanar da karin mutum 12 da suka kamu a daren Laraba.
A daren Larabar ne 15 ga Afrilun 2020, NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane 34 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.
Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na zauren sada zumunta da cewa: “An samu karin mutane talatin da hudu (34) sun kamu da kwayar cutar covid-19 a jihohin Najeriya daban-daban kamar haka; 18 a Legas, 2 a Katsina, 12 a Kano, 1 a Delta, da 1 a Neja."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng