Yaki da ta’addanci: A yau za’a gurfanar da mayakan Boko Haram 58 gaban kotu

Yaki da ta’addanci: A yau za’a gurfanar da mayakan Boko Haram 58 gaban kotu

An kammala shirin gurfanar da mayakan Boko Haram guda 58 gaban wata kotun kasar Chadi domin fuskantar tuhume tuhumen ta’addanci da gwamnatin kasar ke zarginsu dasu.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ta ruwaito ministan sharia na kasar Chadi, Mai Sharia Djimet Arabi ya bayyana cewa Sojojin Chadi sun kamo yan ta’addan ne bayan wani arangama.

KU KARANTA: Coronavirus: Buhari ya zaftare kashi 9.1 daga farashin takin zamani don taimaka ma manoma

Shugaban kasar Chadi, Idris Deby ya bayyana sun fatattaki mayakan Boko Haram daga kasar bayan wani samame da suka kaddamar a ranakun 31 ga watan Maris da 8 ga watan Afrilu.

Kaakakin Sojin Chadi yace sun kashe yan ta’adda 1,000 yayin da Sojoji 52 suka rigamu gidan gaskiya a yayin arangamar, samamen ya auku ne karkashin jagorancin shugaba Idris Deby.

Bayan nasarar da suka samu a wannan hari, Deby ya shaida ma kasashen yankin tafkin Chadi cewa kasarsu ba zata sake shiga yaki da Boko Haram ba matukar ba’a cikin kasarta take ba.

Chadi na cikin kasashen kawance dake yaki da Boko Haram, tare da kawayenta kamarsu Najeriya, Kamaru da Nijar.

Yaki da ta’addanci: A yau za’a gurfanar da mayakan Boko Haram 58 gaban kotu
Yaki da ta’addanci: A yau za’a gurfanar da mayakan Boko Haram 58 gaban kotu
Asali: Twitter

A hannu guda kuma babban hafsan rundunar Sojan kasa ta Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya koma jahar Borno domin fafatawa a yaki da Boko Haram.

Buratai ya dauki alwashin ba zai koma Abuja ba sai sun samu galaba a kan kungiyar Boko Haram tare da tabbatar da sun murkushe ta.

A wani labarin kuma, Akalla mutane 17 ne suka mutu yayin da jirgin yakin Najeriya ya jefa bamabamai a kauyen Sakotoku dake karamar hukumar Dambo ta jahar Borno, bisa kuskure.

Jaridar TheCable ta ruwaito yawancin wadanda suka mutu a harin sune mata da kuma kananan yara, wanda suke wasa da zaman shan iska a karkashin wata bishiyar mangwaro.

Majiyoyi sun bayyana dalilin jefa bamabaman shi ne an sanar da Sojojn sama cewa mayakan Boko Haram na taruwa a kauyen a ranar Alhamis, don haka ta shirya musu luguden wuta.

Inda ya kamata a kai harin shi ne wani yanki a Korongilum dake makwabtaka da Sakotoku da kimanin nisan kilomita 12, a nan ne mayakan Boko Haram din suka taru.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel