Sule Lamido ya bayyana sakamakon gwajin da aka masa a kan COVID-19

Sule Lamido ya bayyana sakamakon gwajin da aka masa a kan COVID-19

Tsohon gwamnan jahar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana sakamakon gwajin da aka masa a kan annobar Coronavirus a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Facebook.

Lamido ya bayyana cewa sakamakon gwagin ya fito, kuma ya nuna baya dauke da cutar Coronavirus, kamar yadda cutar bata kama direbansa da jami’in tsaronsa ba.

KU KARANTA: Coronavirus: Buhari ya zaftare kashi 9.1 daga farashin takin zamani don taimaka ma manoma

“Da misalin karfe 5:35 na yammacin Laraba, 15 ga watan Afrilun 2020 Dakta Imam Wada Bello ya kira ya shaida min cewa sun kammala bincike a kan abubuwan gwajin da suka amsa daga wajenmu.

“Sakamakon gwajin ya nuna ni da direbana da jami’in tsarona duka bama dauke da cutar, sa’annan yace zai turo min da cikakken bayani game da gwajin da suka yi.” Inji Lamido.

Sule Lamido ya bayyana sakamakon gwajin da aka masa a kan COVID-19
Sule Lamido ya bayyana sakamakon gwajin da aka masa a kan COVID-19
Asali: UGC

Lamido yayi mamakin yadda jama’a suka nuna damuwa da halin da yake ciki, tun daga dubun dubatan addu’o’in da masoya da magoya baya suka yi masa ta Facebook da sakon kar ta kwana.

“Allah ne kadai ya san dalilin irin wannan soyayyar da aka nuna min, a yanzu haka bani da wasu kalaman da zan yi don nuna godiya ga kaunar da aka nuna min.

“Fatana Allah Ya yi muku albarka, ya saka muku da alheri, kuma ya kareku daga dukkan wani sharri.” Inji shi.

A wani labari kuma, Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya taya jama’an garin Chibok alhinin cika shekaru 6 tun bayan da mayakan Boko Haram suka sace yan matan.

Wannan tasa gwamnan ya tura kwamishinoni domin wakiltarsa wajen jajanta ma iyayen yan matan da yan uwansu, tare da taya su alhinin rashi, sa’annan kuma ya basu sako su kai musu.

Kwamishinonin sun hada da na ilimi, harkokin mata, rage talauci da mai wakiltar Chibok a majalisar dokokin jahar Borno, kuma sun isar da sakon gwamnan ga iyayen yan matan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng