Yanzu-yanzu: An samu sabbin mutane 34 sun kamu da Coronavirus, 12 a Kano

Yanzu-yanzu: An samu sabbin mutane 34 sun kamu da Coronavirus, 12 a Kano

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane34 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Laraba, 15 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An samu karin mutane talatin da hudu (34) sun kamu da #COVID19;

18 a Lagos

2 a Katsina

12 a Kano

1 a Delta

1 a Neja

Duk a yau, an sallami mutane 28, kuma 2 sun rigamu gidan gaskiya.

KU KARANTA: Coronavirus: Har yanzu ban warke ba - Gwamna El-Rufai

Ga jerin jiha-jiha:

Lagos- 232

Abuja - 58

Osun - 20

Kano- 16

Edo- 15

Oyo- 11

Ogun- 9

Katsina- 7

Bauchi- 6

Kaduna- 6

Akwa Ibom- 6

Kwara- 4

Delta- 4

Ondo- 3

Enugu- 2

Ekiti- 2

Rivers-2

Niger- 2

Benue- 1

Anambra- 1

A bangare guda, Ministan labarai, Lai Mohammed, ya ce gwamnatin tarayya ba zata iya raba wa yan Najeriya kudaden tallafi da hukumomi masu zaman kansu suka bayar don yakar cutar coronavirus ba.

A cewar NAN, ministan ya bayar da dalilan da yasa ba za a ba al’umman kasar kudin ba, a lokacin da ya bayyana a shirin “Politics Nationwide”, na Radio Nigeria a ranar Talata.

Ya yi martani ne ga wata bukata da ke naman a raba wa yan Najeriya wani bangare na kudaden domin su toshe gibin da dokar hana fita ya yi masu.

Ministan ya ce kudaden na inganta harkar lafiya ne, sannan cewa ba za a iya amfani dashi wajen samar da kayan rage radadi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel