COVID-19: FG ta bayyana gaskiyar lamari a kan lafiyar likitocin China da suka zo Najeriya

COVID-19: FG ta bayyana gaskiyar lamari a kan lafiyar likitocin China da suka zo Najeriya

- Gwamnatin tarayya ta ce babu daya daga cikin ma'aikacin lafiyar kasar China da suka zo a makon da ya gabata mai dauke da cutar coronavirus

- A ranar Larabar makon da ya gabata ne ma'aikatan lafiya 15 daga kasar China suka iso Najeriya dauke da kayayyakin asibiti na a kalla dala miliyan daya da rabi

- Ya kara da musanta rahoton cewa 'yan majalisar dattijan kasar nan sun raba wasu makuden kudade tsakaninsu don yakar annobar Coronavirus

Gwamnatin tarayya ta ce babu daya daga cikin ma'aikacin lafiyar kasar China da suka zo a makon da ya gabata mai dauke da cutar coronavirus.

A ranar Larabar makon da ya gabata ne, ma'aikatan lafiya 15 daga kasar China suka iso Najeriya dauke da kayayyakin asibiti na a kalla dala miliyan daya da rabi.

Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya sanar da hakan a jiya Laraba a garin Abuja.

Ya kara da cewa zantuka na bogi kuma marasa tushe game da annobar nan basu da dadin sauraro.

Ya kara da musanta rahoton cewa 'yan majalisar dattijan kasar nan sun raba wasu makuden kudade tsakaninsu don yakar annobar Coronavirus.

COVID-19: FG ta bayyana gaskiyar lamari a kan lafiyar likitocin China da suka zo Najeriya

COVID-19: FG ta bayyana gaskiyar lamari a kan lafiyar likitocin China da suka zo Najeriya
Source: UGC

KU KARANTA: COVID-19: Yadda wasu mayunwatan 'yan Najeriya suka doka wa motar biredi da shinkafa wawaso (Bidiyo)

Kamar yadda yace, kwamitin shugaban kasa na yakar muguwar cutar ba ya sauraron labaran bogi, domin suna dauke musu hankali tare da gwamnati wajen yakar annobar.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su saki duk wani rahoto game da gwamnati wanda zai iya hana yakar annobar, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Dukkan labarai da basu fito daga bakin kwamitin shugaban kasar ba ko shafin yanar gizo na NCDC, toh abin gujewa ne.

"A yayin da muke kokarin yakar annobar Coronavirus, akwai bukatar yakar labaran bogi. Ni dai ban san labarin komai a kan kudin da ake cewa 'yan majalisar tarayya na rabawa tsakaninsu ba.

"Da safiyar nan, akwai labarin da ke ta yaduwa mai cewa daya daga cikin likitocin kasar China da suka zo Najeriya yana dauke da cutar.

"Wannan labarin ba gaskiya bane kuma kamata yayi ku ji daga wajen gwamnati. Ina so in tabbatar muku da cewa ba gaskiya bane," Mohammed yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel