An gano sabbin nau'ikan coronavirus shida a jikin jemagu a Myanmar

An gano sabbin nau'ikan coronavirus shida a jikin jemagu a Myanmar

A yayin da duniya ke kokarin dakile yaduwar kwayar cutar Covid-19 a tsakanin mutane, masu bincike da ke nazari a kan jemagu a Myanmar sun gano sabbin nau'ikan coronavirus guda shida kamar yadda jaridar Metro ta ruwaito.

Wannan shine karo na farko da aka fara gano wadannan sabbin kwayoyin cutar a karkashin shirin Lafiya ta Smithsonian Global Health Program inda masu binciken suka ce ba su da alaka ta kusa da sauran nau'ikan iyalan coronavirus wato covid-19, SARS, MERS da sauran biyun.

Binciken da aka wallafa a mujallar kimiyya ta PLOS ONE an yi ta ne na nufin fahimtar yadda coronavirus ya ke a jikin jemagu.

An gano sabbin nau'ikan coronavirus shida a jikin jemagu a Myanmar

An gano sabbin nau'ikan coronavirus shida a jikin jemagu a Myanmar
Source: UGC

Ana fatan binciken zai yi karin haske game da binciken da masana na duniya ke yi domin gano kwayoyin cutar da ka iya bullowa a gaba da kuma yadda alumma za su magance su.

DUBA WANNAN: An kama wadanda aka killace saboda coronavirus suna zina da juna

Marc Valitutto, tsohon likitan dabobin daji da ke aiki da Smithsonian Global Health Program kuma jagoran masu binciken ya ce, "Annoba tana tunatar da mu yadda lafiyar mutane ke da kusanci da na dabobi."

Za mu fi iya kare yaduwar cututtuka da annoba idan muka fahimci yadda kwayoyin cuta suke a jikin dabobin daji da yadda suke rikide wa su shiga wasu jinsosi kamar mutane, a cewar Valitutto.

Masu binciken sun gano wadannan sabbin kwayoyin cutar ne yayin da suke nazarin dabobi da nuffin zurfafa fahimtar su kan yadda cututtuka ke yaduwa tsakanin dabobi da mutane a karkashin wani shiri mai suna Predict.

Hukumar Raya Kasashe ta Amurka, USAID, ne ta dauki nauyin wannan bincike a kan kwayoyin cutar da ke iya haifar da annoba a duniya.

Masu binciken sun mayar da hankali a Myanmar ne saboda mutanen kasar suna yawan cudanya da dabobin daji a sakamakon sabbin gidaje da ake gina wa don fadada birane.

Kazalika, sun ce kwayoyin hallita da dama a karkashin coronavirus ba su cutar da mutane amma idan an gano su a jikin dabobbi za a samu daman yin nazari a kan yiwuwar yaduwar su zuwa mutane da cutar da su a cewar Suzan Murray.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel