NLC ta yaba ma Ganduje game da matakin sanya ma jama’an takunkumi da ya dauka

NLC ta yaba ma Ganduje game da matakin sanya ma jama’an takunkumi da ya dauka

Kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC, ta yaba da matakin garkame jahar Kano tare da sanya takunkumi ga al’ummar jahar domin kare yaduwar cutar Coronavirus a jahar.

Shugaban NLC reshen jahar Kano, Kabir Ado-Minjibir ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, a ranar Laraba.

KU KARANTA: Ministar Buhari ta bayyana iya adadin yan Najeriya da zasu amfana da tallafin gwamnati

A cewar Ado, NLC bata adawa da duk wani mataki da gwamnati za ta dauka domin kare yaduwar annobar Coronavirus a jahar Kano, asali ma tana goyon bayan ire iren matakan.

“Muna kuma kira ga hukumomin tsaro su mutunta ma'aikata, musamman masu gudanar da muhimman aiki, kamar jami’an kiwon lafiya da yan jaridu, kuma suma jami’an namu su tabbata suna amfani da tufafin da ya kamata da kuma sahihin shaida.

NLC ta yaba ma Ganduje game da matakin sanya ma jama’an takunkumi da ya dauka
NLC ta yaba ma Ganduje game da matakin sanya ma jama’an takunkumi da ya dauka
Asali: Twitter

“Muna kira ga duk ma’aikatan jahar Kano wadanda ba’a bukatar aikinsu a yanzu su cigaba da zamansu a gida don yin biyayya ga umarnin gwamnati domin tabbatar da kare lafiyar al’ummar jahar.” Inji shi.

Daga karshe Ado ya yi fatan Allah Ya sa dokar ta yi sanadiyyar dakatar da yaduwar cutar bayan kwanaki 7 da gwamnatin ta diba, sa’annan ya yi fatan Allah Ya ba wadanda suka kamu lafiya.

A wani labari kuma, Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta rage farashin takin zamani samfurin NPK da kashi 9.1 domin taimaka ma manoma.

Jaridar TheCables ta ruwaito gwamnan jahar Jigawa, Muhammadu Badaru ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Dutse a ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu.

Gwamna Badaru, wanda yake shugabantar kwamitin shugaban kasa a kan harkar taki, PFI, ya ce gwamnatin ta dauki wannan mataki ne a matsayin tallafi ga yan kasa.

Gwamnatin ta rage 9.1% daga farashin buhun takin NPK mai nauyin kilo 50, a yanzu dai buhun NPK ya kai N5,500, amma sakamakon wannan ragin kashi 9.1, farashin ya dawo N5,000 kacal.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel