Yanzu-yanzu: An sallami mutane 22 daga asibiti bayan sun warke daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 22 daga asibiti bayan sun warke daga Coronavirus

An sallami masu cutar Coronavirus 22 da sukayi jinya a jihar Osun da Legas bayan gwaji biyu daban-daban ya nuna cewa sun warke daga cutar.

Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya bayyana cewa a jiharsa, sun sallami mutane shida.

Amma na Legas, Babajide Sanwoolu, ya bayyana cewa mutane 16 suka sallama ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu, 2020.

Gwamnan jihar Legas yace: “Ina da karin labari mai dadi daga cibiyoyin killacewanmu. Mun sallami mutane 16; maza 14, mata 2.“

“Daga cikinsu akwai Turawa 3 - Dan Birtaniya 1, dan China 1 da dan Poland daya.“

“Hakan ya kawo adadin mutanen da muka yi jinya kuma muka sallama zuwa 85.“

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 7 daga asibiti a Osun bayan sun warke daga Coronavirus

Coronavirus
Source: Depositphotos

KU KARANTA COVID-19: Ganduje ya bada umarnin garkame jihar Kano na sati daya

A bangare guda, Wani kwararren likita, Dr Chinonso Egemba, ya ce masu amfani da man kara hasken fata, ka iya fadawa halin rashin lafiya mai tsanani ko ma su mutu sanadiyar cutar coronavirus.

Egemba, ya fada ma kanfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba, cewa wasu mayun bilicin da sabulu na dauke da sinadarin ‘steroids’, wanda ke rage karfin kariyar da jiki ke dashi.

Ya bayyana garkuwar jiki, a matsayin kariyar da jiki ke dashi wajen yakar kwayoyin cututtuka da ke haifar da coronavirus da sauran kwayoyin halitta da ke taba jikin dan Adam, da wanda yake shaka a kullun.

Yace “Idan kana bilicin, toh ka daina saboda yana rage garkuwar jiki sannan kuma mutane ko marasa lafiya da ke da karancin garkuwar jiki sun fi jin jiki kuma suna iya mutuwa sakamakon cutar.“

“Sinadarin ‘steroids’ su kan kasance magunguna masu hana kumburi, kuma kumburi na daya daga cikin hanyoyin da jikinmu ke zubar da bakin abubuwa. Yana iya kasancewa ta kumburin jiki ko kuma ta marurai ko jajjayen kuraje a jiki.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel