Tunawa da harin Nyanya: Mutane sun koka da rashin kulawar gwamnati

Tunawa da harin Nyanya: Mutane sun koka da rashin kulawar gwamnati

Ranar 14 ga Afrilun 2014, na daya daga cikin ranaku mafi muni a zukatan 'yan Najeriya da ba za a manta da su ba musamman mazauna babban birnin kasar nan wato Abuja.

A wannan rana ce kungiyar yan tayar da kayar baya ta Boko Haram, ta sace 'yan mata 276 na wata makarantar sakandire a garin Chibok a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas.

Kuma wannan rana ce da kungiyar Boko Haram ta kai mummunan harin bam a yankin Nyanya na garin Abuja, inda rayukan mutane fiye da 70 suka salwanta yayin da dama suka jikkata.

An samu salwantar rayuka da dama a sanadiyar yadda a wancan lokaci tashar motar Nyanya ke tara dumbin al'umma kasancewarta cibiyar tatattara matafiya musamman masu karamin karfi.

Jaridar Human Angle ta ruwaito tuni dai mutane suka kauracewa tashar tun bayan aukuwar wannan mummunan harin da ya shata tabo mai girman gaske a zukatansu.

Osinbajo yayin da ya ziyarci kasuwar Nyanya ta Abuja a 2018
Osinbajo yayin da ya ziyarci kasuwar Nyanya ta Abuja a 2018
Asali: Depositphotos

Bayan aukuwar harin ne hukumar kula da birnin Abuja karkashin jagorancin gwamnan Bauchi na yanzu, Bala Muhammad, ta sha alwashin daukar nauyin dukkanin wadanda harin ya shafa.

Wannan alwashi ya sanya tsohon sakataren dindindin na hukumar, Mr John Chukwu, ya jaddada kudirin gwamnati a kan jin kan wadanda ibitila'in ya auku a kansu.

Mr Chuckwu ya bayyana karara cewa, an daukewa wadanda suka jikkata duk wani nauyi na kudin kula da na magani a asibitocin da suke jinya a duk fadin Abuja.

Shekaru shida kenan bayan aukuwar harin, wadanda ibtila'ain ya auku a kansu sun ce kawowa yanzu, babu ko alkawari daya da gwamnatin ta cika, lamarin da suka ce duk kanzon kurege ne.

Daya daga cikinsu Mista Celestine Anaigbo, ya ce an yi masa aikin tiyata kashi-kashi tun bayan da azal din ta auku a kansa ba tare da samun wani tallafi daga gwamnati ba.

Anaigbo ya ce, haka nan gwamnati tayi watsi da shi a asibitin da yake jinya, lamarin da dole ta sanya ya nemi taimakon 'yan uwa, makusanta da abokanan arziki.

Ya ce "sai da na kashe naira miliyan uku domin yi min aiki har sau biyu a kafafu na a asibitin Cedar Crest, kuma har yanzu zan koma domin kuwa akwai karashen aikin.

"Na nemi taimako ta hanyar shigar da muryata wajen kai koke a gidajen radiyo amma lamarin yaci tura."

"A halin yanzu ina neman wata naira miliyan ukun domin samun damar a karasa min aiki, amma bani da hali."

KARANTA KUMA: Najeriya ta bayyana rashin jin dadi kan cin zarafin 'yan kasarta a China saboda coronavirus

Haka kuma wata mata, Prisalia Chinadu, ta ce ita ta daukin nauyi biyan kudin magani a babban asibitin Nyanya inda ta yi jinya bayan harin ya ritsa da ita.

Chinadu ta ce an mayar da ita asibitin Gwagwalada Specialist, inda ta ci gaba da jinya da taimakon 'yan uwanta da makusanta.

Har ila yau wata mata Christiana Agbo, ta ce bayan da gwamnati tayi watsi da ita, dole ta sanya 'yan uwanta suka mayar da ita gida inda aka yi jinyarta ta hanyar shan magungunan gargajiya.

Bugu da kari wasu mata biyu da suka rasa mazajensu a harin, Favour Ndubisi da kuma Sarah Andy, sun kirayi gwamnati a kan ta kawo masu agaji domin ci gaba da dawainiya da yaransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel