Yanzu-yanzu: Adadin wadanda suka kamu da Coronavirus a duniya ya kai miliyan biyu
Adadin wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a fadin duniya ya zarce miliyan biyu bayan makonni biyu kacal da cika miliyan daya.
A wannan makon akayi kwana dari da bullar cutar a duniya.
Lissafi daga jami'ar Johns Hopkins dake kasar Amurka da ke bibiyan adadin mutane ya nuna cewa mutane 2,000, 984 ne suka kamu da cutar kawo karfe 3:30 na ranar Laraba, 15 ga Afrilu, 2020.
Yayinda mutane 493, 658 suka samu warkewa daga cutar bayan jinya a asibiti, mutane 128, 071 sun rigamu gidan gaskiya.
Zaku tuna cewa ranar 2 ga Afrilu 2020 muka kawo muku rahoton cewa adadin wadanda suka kamu da cutar a duniya ya kai miliyan daya.
A lokacin, mutane 208,949 ne suka warke yayinda 51,945 suka mutu.
Idan akayi lissafi, za a gana cewa cikin kwanaki 12, an samu karin mutane milyan daya da suka kamu, 284,709 sun warke, kuma 76,126 suka mutu.
Cikin kwanakin nan, kasar Amurka, Ingila, Faransa, Italiya, da Andalus ne suka fuskanci fushin annobar Coronavirus.
KU KARANTA An sallami mutane 7 daga asibiti a Abuja bayan sun warke daga Coronavirus

Asali: Facebook
Kasashen da ke kan gaba wajen yawan masu cutar sune:
Amurka - 609,696
Sifen -177,633
Italiya - 162,488
Jamus - 132,321
Faransa - 131,362
Birtaniya 94,852
Sin - 83,355
Iran - 50,468
A nan gida Najeriya kuwa, A sallami karin mutane tara daga cibiyar killacewa da jinyar masu cutar Coronavirus dake asibitin koyarwan jami'ar Abuja dake Gwagwalada, birnin tarayya Najeriya.
Hakan ya kawo adadin wadanda aka sallama a Abuja kawo yanzu 18.
Rahoton ya bayyana cewa an sallamesu ne a daren Talata bayan sun cika dukkan sharrudan sallama kuma sakamakon gwajinsu biyu daban-daban sun fito kuma sun tabbatar sun barranta.
Sashen yada labaran hukumar cigaban birnin tarayya ta bayyana hakan a wasikar da ta saki.
Har yanzu babu labari akn shugaban maaikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, tun bayan komawarsa Legas.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng