Rabon tallafi saboda annobar covid-19: FG ta sauya salo

Rabon tallafi saboda annobar covid-19: FG ta sauya salo

Gwamnatin tarayya (FG) ta sanar da samar wasu sauye - sauye a salon rabon tallafin jin kai da ta ke bawa talakawa da marasa karfi domin rage musu radadin matsin tattalin arziki da annobar cutar covid-19 ta haifar.

FG ta bayyana cewa za ta fara duba asusun bankin jama'a da kudin da suke kashewa wajen sayen katin waya domin sanin su waye ya dace ta bawa tallafinta na jin kai a zagaye na biyu na bayar da tallafin.

A cewar FG, duk wani dan Najeriya da ya ke da kudin da yawansu ya kai N5,000 a cikin asusunsa na banki ba zai samu tallafinta na jin kai da za ta raba a zagaye na biyu ba.

Kazalika, gwamnatin ta bayyana cewa akwai yiwuwar ba za ta bayar da tallafinta ga duk mai saka katin waya na fiye da N100 ba a rana.

A cewar ministar jin dadi da walwalar jama'a, Sadiya Umar Farouq, rabon tallafin jin kai zagaye na biyu zai mayar da hanakaline a kan talakawa da marasa karfi da ke zaune a kauyuka da maraya.

Rabon tallafi saboda annobar covid-19: FG ta sauya salo

Rabon tallafin kudi a Abuja
Source: Twitter

Ministar ta bayyana cewa gwamnati za ta mayar da hankali a kan ma su bukata ta musamman yayin rabon tallafin.

DUBA WANNAN: FG ta janye shirin bayar da tallafin N20,000 a jihohi hudu

Da ta ke amsa tambaya a kan hanyar da gwamnati za ta bi wajen zakulo mutanen da su ka dace a bawa tallafin, ministar ta bayyana cewa gwamnati za ta yi amfani da lambar tantance asusun banki (BVN) da kuma layin wayar hannu na jama'a.

A wani jawabi da ta gabatar ranar Litinin, ministar ta bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarni a kara adadin mutum miliyan daya a kan wadanda suka ci moriyar tallafin a zagaye na farko.

Tsarin shirin bayar da tallafin jin kai da gwamnatin tarayya ta fara ya na shan suka a wurin jama'a tare da saka babbar ayar tambaya a kan salon rabon tallafin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel