Yanzu-yanzu: An sake mutuwa sakamakon COVID-19 a Legas

Yanzu-yanzu: An sake mutuwa sakamakon COVID-19 a Legas

- A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Legas ta sanar da mutuwar wani majiyanci daya sakamakon muguwar annobar coronavirus

- Ma'aikatar lafiya ta jihar Legas din ta sanar da hakan ne ta shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta twitter

- Gwamnatin jihar ta sake sanar da sabbin masu cutar har 25, hakan ne ya kai jimillar masu cutar a jihar har 217

A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Legas ta sanar da wani majiyanci daya da ya rasa ransa sakamakon muguwar annobar coronavirus.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, wannan ya faru ne kasa da sa'o'i 24 da aka rasa majinyaci daya sakamakon muguwar cutar.

Gwamnatin jihar ta sake sanar da sabbin masu cutar har 25. Hakan ne ya kai jimillar masu cutar a jihar har 217.

Ma'aikatar lafiya ta jihar Legas din ta sanar da hakan ne ta shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta twitter.

Ma'aikatar lafiyar dai bata bada cikakken bayani game da majiyacin da ya rasu ba.

"A ranar 14 ga watan Afirilun 2020, mutane 25 ne suka sake kamuwa da muguwar cutar, hakan ya kai jimillar masu cutar a jihar ya kai 217.

"Mutane takwas; mata biyu da maza shida aka sallama bayan jinyar cutar coronavirus. wadanda aka sallama sun kai 69," aka wallafa a shafinta na twitter.

Yanzu-yanzu: An sake mutuwa sakamakon COVID-19 a Legas

Yanzu-yanzu: An sake mutuwa sakamakon COVID-19 a Legas
Source: UGC

KU KARANTA: COVID-19: Yadda wasu mayunwatan 'yan Najeriya suka doka wa motar biredi da shinkafa wawaso (Bidiyo)

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, mutane 30 suka sake kamuwa da cutar a ranar 14 ga watan Afirilun 2020.

Wannan ne mutane mafi yawa da suka taba kamuwa da cutar a rana daya tun bayan shigowarta kasar nan.

A halin yanzu, mutane 373 ne suka kamu da cutar a jihar, mutane 274 ke jinya yayin da aka sallama mutane 99 daga asibiti.

Majinyata biyu ne aka mayar kasarsu yayin da wasu ukun aka mayar da su jiharsu ta asali.

A nan Arewa kuwa, gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa masu dauke da muguwar cutar sun kai 9 a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel