Barazanar Kyanda ka iya biyo bayan cutar corona - UNICEF

Barazanar Kyanda ka iya biyo bayan cutar corona - UNICEF

Jami'ai sun ce cutar kyanda na iya barkewa a sanadiyar yadda aka karkatar da akalar kulawa wajen yakar annobar cutar corona virus da ta karade ko ina a fadin duniya.

Majalisar Dinkin Duniya karkashin asusun kula da tallafawa kananan yara, UNICEF, ta ce akalla yara miliyan 117 cikin kasashe 37 ka iya rasa samun allurar rigakafin cutar kyanda a kan lokaci.

UNICEF ta ce barazanar wannan lamari ta tunkaro da dama daga cikin kasashe a sanadiyar yadda aka bayar da mafi rinjayen hankali wajen yakar cutar corona da ta hana ruwa gudu.

Ta ce ana iya samun barkewar cutar kyanda a sanadiyar kakagidan da cutar corona tayi saboda yadda ake tsaikon gudanar da shirin allurar rigakafin cututtuka da suka sanya bil Adama a gaba.

Babu shakka an samu karuwar barkewar cutar corona a kasashen duniya musamman nahiyyar Turai inda allurar rigakafin ta yi karanci.

Allurar rigakafin cutar kyanda
Allurar rigakafin cutar kyanda
Source: Depositphotos

BBC ta ruwaito cewa, a halin yanzu tuni kasar Birtaniya ta gurbata da masu cutar kyanda biyo bayan tsarkakuwa daga cutar da ta rasa a sanadiyar ci gaba da yaduwar annobar corona.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce kasashen da suka tsarkaka daga cutar kyanda a yanzu ka iya tafiya wani ɗan takaitaccen hutu na dakatar da allurar rigakafi matukar akwai bukatar hakan.

Sai dai ta ce kasashe 24 da ke fafutikar yakar barkewar cutar kyanda sun dakatar da shirin allurar rigakafin cutar a sanadiyar bullar annobar corona da ta dagula lamurra a duniya baki daya.

Jerin kasashe 24 da cutar kyanda ta yiwa lullubi a yanzu sun hada da Bangladesh, Brazil, Bolivia, Cambodia, Chadi, Chile, Columbia, Djibouti, Jamhuriyyar Dominican, Ethiopia, Honduras da Nepal.

Sauran kasashen sun hada da; Jamhuriyyar Congo, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Lebanon, Maldives, Mexico, Paraguay, Somaliya, Ukraine, Uzbekistan, Sudan ta Kudu da kuma Najeriya.

KARANTA KUMA: Covid-19: Gwamnatin Bauchi ta dakatar da tatsar albashin ma'aikata

Mai magana da yawun WHO, Joanna Rea, ta kara da cewa, "dakatar da allurar rigakafin za ta haifar da karuwar adadin yara da za su kamu da cutar, lamarin da zai jefa mahukuntan lafiya a fadin duniya cikin wani sabon rudani."

Dakta Mary Ramsay, shugaba ta reshen allurar rigakafi a kasar Ingila, ta yi gargadin cewa "an samu nasarori da dama wajen aiwatar da alluran rigakafin miyagun cututtuka kama daga sankarau, tarin fika da sauransu."

Alkalumma sun tabbatar da cewa, cutar kyanda a kowacce shekara ta na kama yara miliyan 20 ko fiye da haka a sassan duniya duk da rahusa da kuma wadatuwar maganinta.

Legit.ng ta fahimci cewa, cutar kyanda ta kashe yara dubu 140 wadanda galibinsu ba su haura shekaru biyar da haihuwa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel