An kama wadanda aka killace saboda coronavirus suna zina da juna

An kama wadanda aka killace saboda coronavirus suna zina da juna

- Babbar sakatariyar ma'aikatar lafiya ta kasar Uganda ta bayyana cewa wasu wadanda aka killace a dakunan otal na zina da junansu

- Ta ce wannan lamarin zai kasance babban koma baya da zagon kasa ga kokarin gwamnatin kasar na yakar yaduwar cutar coronavirus

- Babbar sakatariyar ta bayyana cewa, ganin hakan ne yasa suka kasa sallamar duka wadanda ke killace a kasar har yanzu

Babban sakatariyar ma'aikatar lafiya ta kasar Uganda ta bayyana cewa mutanen da aka killace a waje daya a kasar na neman juna don jima'i, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Kamar yadda babban sakatariyar ta bayyana a wata hira da aka yi dashi a gidan rediyo, da yawa daga cikin wadanda aka killace a otal suna zuwa wasu dakunan don samun wadanda za su kwanta dasu.

Ta ce hankalin ma'aikatar lafiya tayi matukar tashi a kan wannan lamarin na zagon kasa ga kokarin gwamnatin tarayyar wajen hana yaduwar cutar coronavirus a Uganda.

"Yan kasar Uganda basu da lissafi. Wasu da aka killace sun fara kwanciya da juna. Suna yawo cikin dakunan otal din da aka killacesu. Wani ziyara yake kaiwa abokan aikinsa da aka killacesu a otal daya," tace.

Covid-19: An kama wadanda aka killace suna zina da juna

Covid-19: An kama wadanda aka killace suna zina da juna
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Shekau ya fadi maganin coronavirus a cikin sabon sakon sautin murya da ya fitar

Kamar yadda ta kara da cewa, "Wannan lamarin na da matukar hatsari kuma ya zama koma baya ga kokarinmu".

Kamar yadda tace, wannan dalilin ne yasa suka ki sallamar mutane tun bayan da aka gano cewa ga abinda suke aikatawa.

An gano wannan lamarin ne makonni kadan bayan ma'aikatar lafiyar kasar ta sanar da cewa an ware wurare 17 don amfani dasu a matsayin cibiyar killacewa.

Wadannan wuraren sun hada da dakunan otal, asibitoci, masaukin baki da jami'o'i inda aka killace a kalla mutane 232.

Uganda na da a kalla mutum 50 da aka tabbatar suna dauke da muguwar cutar, amma mutum 7 ne suka warke daga cutar.

Har yanzu dai cutar na ci gaba da fadawa kasashen nahiyar Afirka tare da kwashe rayuka. Amma babbar barnar da muguwar annobar tayi yana nahiyar Turai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel