Yanzu-yanzu: An sallami mutane 9 daga asibiti a Abuja bayan sun warke daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 9 daga asibiti a Abuja bayan sun warke daga Coronavirus

A sallami karin mutane tara daga cibiyar killacewa da jinyar masu cutar Coronavirus dake asibitin koyarwan jami'ar Abuja dake Gwagwalada, birnin tarayya Najeriya, Rahoton DailySun.

Hakan ya kawo adadin wadanda aka sallama a Abuja kawo yanzu 18.

Rahoton ya bayyana cewa an sallamesu ne a daren Talata bayan sun cikka dukkan sharrudan sallama kuma sakamakon gwajinsu biyu daban-daban sun fito kuma sun tabbatar sun barranta.

Sashen yada labaran hukumar cigaban birnin tarayya ta bayyana hakan a wasikar da ta saki.

Jawabin yace “Muna farin cikin sanar muku da cewa an sallami marasa lafiya bakwai daga cibiyar killace mutane a asibitin koyarwan jami'ar Abuja UATH.“

“Sauran na cikin isasshen lafiya kuma suna samun sauki. Muna godiya ga Allah.“

Gabanin yanzu, an sallami mutane 11 kuma ana kyautata zaton za a sallami sauran nan ba da dadewa ba.

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 7 daga asibiti a Abuja bayan sun warke daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 7 daga asibiti a Abuja bayan sun warke daga Coronavirus
Source: Depositphotos

KU KARANTA Shekau ya fadi maganin coronavirus a cikin sabon sakon sautin murya da ya fitar

Cikin awanni 24, Cibiyar Takaita Yaduwar Cututtuka ta Najeriya, NCDC, a jiya ta tabbatar da sabbin mutane 3O da suka kamu da coronavirus a kasar wadda hakan ya kawo jimillar masu cutar a kasar zuwa 373.

Mutum 11 ne kuma cutar ya kashe a kasar a halin yanzu.

A cewar hukumar ta NCDC, "Kawo yanzu an tabbatar da masu cutar 373, 99 sun warke an sallame su yayin da mutane 11 sun mutu sakamakon cutar a Najeriya."

A fadin duniya kuwa, an gwada mutane 3,120,381. yayinda mutane 1,996,681 suka kamu da cutar, 127, 590 sun rigamu gidan gaskiya.

Kasar Amurka ke kan gaba waen yawan wadanda suka kamu da cutar.

A bangare guda, gwamnatin tarayya (FG) ta sanar da cewa ta gimtse shirin bayar da tallafin jin kai a jihohin Najeriya guda hudu.

A cewar wani jawabi da ministar jin dadi da walwala, Sadiya Umar Farouq, ta fitar ranar Talata, ta bayyana cewa an janye shirin daga jihohin ne saboda saba ka'idojin yarjejeniyar bayar da tallafin da 'yan kwangila suka yi a jihohin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel