COVID-19: Yadda wasu mayunwatan 'yan Najeriya suka doka wa motar biredi da shinkafa wawaso (Bidiyo)

COVID-19: Yadda wasu mayunwatan 'yan Najeriya suka doka wa motar biredi da shinkafa wawaso (Bidiyo)

- A yayin da dokar kulle ta ci gaba a jihohin Abuja, Ogun da Legas, wasu bidiyo sun fara yawo a kafafen sada zumuntar zamani

- A bidiyon dai an ga wasu mayunwatan 'yan Najeriya na doka wawaso a kan motocin da ke dauke da shinkafa da biredi a jihar Legas

- Bidiyon ya jawo cece-kuce daga ma'abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani inda suke zargin cewa yunwa ce ta gallabi 'yan Najeriyan

A yayin da dokar kulle ta ci gaba a jihohin Abuja, Ogun da Legas, wani bidiyo sun fara yawo a kafafen sada zumuntar zamani.

A bidiyon dai an ga wasu mayunwatan 'yan Najeriya na doka wawaso a kan motocin da ke dauke da shinkafa da biredi a jihar Legas.

An gano cewa motocin sun je kai tallafin kayan abinci ne kamar yadda gwamnati tayi alkawari.

Bidiyon ya jawo cece-kuce daga ma'abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani inda suke zargin cewa yunwa ce ta gallabi 'yan Najeriyan.

Wasu kuwa sun yi amfani da wannan damar ne ta hanyar ambaton masu ruwa da tsaki a harkar rabon wadanda suka hada da shugaban kasa, don ankarar da su abinda ke faruwa.

Ana zargin cewa rashin kaiwar kayayyakin tallafin inda ya kamata ne ya jawo wannan al'amarin.

KU KARANTA: Tirsasa mu aka yi muka sadaukar da albashinmu na wata biyu - Dan majalisar tarayya ya fasa kwai

A wani labari na daban, an ji cewa dan majalisar wakilai mai suna Abubakar Lado Abdullahi Suleja, ya ce shi da sauran 'yan majalisar wakilai sun hakura da albashinsu don yakar COVID-19 ne ba don son ransu ba.

Dan majalisar ya sanar da hakan ne a hira da aka yi dashi a gidan rediyon da ke mazabarsa.

Ya ce an tirsasasu hakura da albashinsu ne na watanni biyu ba da son ransu ba, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Lado wanda ke wakiltar mazabar Guevera/Suleja/Tafa, ya ce duk da ya hakura da albashinsa ba da son ransa ba, ya taimakawa jama'ar mazabarsa mabukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel