Gwamnatin Legas ta gano sabbin mutane 119 dake dauke da alamomin COVID-19

Gwamnatin Legas ta gano sabbin mutane 119 dake dauke da alamomin COVID-19

Gwamnatin jahar Legas ta bayyana cewa ta gano wasu sabbin mutane 119 dake dauke da alamomin annobar cutar Coronavirus, watau COVID-19 mai toshe numfashi.

Jaridar Punch ta ruwaito kwamishinan kiwon lafiya na jahar Legas, Farfesa Akin Abayomi ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Talata, 14 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Jimamin shekara 6 da sace yan matan Chibok: Zulum ya yi ma iyayensu kabakin alheri

A cewar Abayomi, sun gano mutanen ne yayin binciken gida gida da suka kaddamar domin kiyaye yaduwar cutar a tsakanin al’umma, inda suka shiga gidaje 118,000 zuwa yanzu.

“Mun kaddamar da bi gida gidan ne tare da jami’an kiwon lafiya don shiga lunguna da sakon yankunan da muke zargin cutar ta fi kamari, a cikin kwanaki 2 mun shiga gidaje 118,000 muna neman masu dauke da manyan alamomin COVID-19.

Gwamnatin Legas ta gano sabbin mutane 119 dake dauke da alamomin COVID-19
Akin Abayomi
Asali: Twitter

“A haka muka samu mutane 119 dake dauke da alamomin. Amma ya kamata a sani COVID-19 daya ne daga cikin cututtukan dake kawo wahalar numfashi, don haka basu kadai bane, shi yasa muke yi ma mutanen gwaji don sanin matsayinsu.” Inji shi.

Daga karshe Abayomi yace daga sakamakon gwajin ne suke gane iya tsanantar cutar COVID-19 a unguwannin da suka shiga.

Jahar Legas ce dai kan wajen yawan adadin masu dauke da cutar Coronavirus, inda take da mutane 214 da annobar ta kama yayin da mutane 10 suka mutu a jahar duk a sanadiyyar cutar.

A wani labarin kuma, Alkalumma daga kamfanin dillancin labarun AFP sun nuna Coronavirus ta kashe fiye da mutane 120,000 zuwa karfe 12 na ranar Talata, 14 ga watan Afrilun 2020.

Alkalumma sun bayyana tun daga watan Disamba da aka samu bullar cutar a China zuwa yau, ta kashe mutane 120,013 inda kashi 70 daga ciki duk yan kasashen Turai ne.

AFP ta ce ta tattara wadannan alkalumma ne daga bayanan da hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO, take fitarwa ne a kullum, wanda ya nuna turawa 81,474 ne suka mutu daga cutar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel