Ana wata ga wata: Zazzabin Lassa ta kashe yan Najeriya 188 yayin da Corona ke ruruwa

Ana wata ga wata: Zazzabin Lassa ta kashe yan Najeriya 188 yayin da Corona ke ruruwa

Jimillan mutane 189 ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar cutar zazzabin Lassa a Najeriya cikin shekara 2020, kamar yadda hukumar kare yaduwar cututtuka, NCDC ta bayyana.

Punch ta ruwaito an samu mace macen ne yayin da duniya ke fama da annobar Coronavirus, inda hukumar NCDC ta ce mutane 189 sun mutu ne daga watan Janairu zuwa Afrilu.

KU KARANTA: Jimamin shekara 6 da sace yan matan Chibok: Zulum ya yi ma iyayensu kabakin alheri

Zazzabin Lassa ana samunsa ne daga abinci ko amfani da kayan amfanin gida da beraye suka yi ma fitsari ko kashi. An fara samun cutar ne a shekarar 1969 a garin Lassa dake jahar Borno.

Cutar Lassa ta fi kamari a tsakanin kasashen Sierra Leone, Liberia, Guninea da kuma Najeriya, inda a Najeriya kadai an samu mutane 963 da suka kamu da cutar a shekarar 2020.

Ana wata ga wata: Zazzabin Lassa ta kashe yan Najeriya 188 yayin da Corona ke ruruwa

Ana wata ga wata: Zazzabin Lassa ta kashe yan Najeriya 188 yayin da Corona ke ruruwa
Source: Twitter

Rahoton ta kara cewa cutar ta watsu a kananan hukumomi 126 a jahohi 27, inda a cikin sati na 14 an samu mutane 19 da suka kamu.

“Daga mako na 1 zuwa na 14 na shekarar 2020, an samu mace mace 188. Haka zalika jahohi 27 sun samu bullar cutar, kimanin mutum 1 kenan a cikin kananan hukumomi 126.” Inji rahoton.

Rahoton ta nuna jahar Edo ne kan gaba da mutane 314, Ondo 309, Ebonyi 73, Taraba 55, Bauchi 43, Kogi 34, Filato 28. Game da mace mace kuwa, jahar Edo tana da 44 yayin da Kaduna ke da 5.

A wani labarin kuma, Alkalumma daga kamfanin dillancin labarun AFP sun nuna cewa Coronavirus ta kashe fiye da mutane 120,000 zuwa karfe 12 na ranar Talata, 14 ga watan Afrilun 2020.

Alkalumma sun bayyana tun daga watan Disamba da aka samu bullar cutar a China zuwa yau, ta kashe mutane 120,013 inda kashi 70 daga ciki duk yan kasashen Turai ne.

AFP ta ce ta tattara wadannan alkalumma ne daga bayanan da hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO, take fitarwa ne a kullum, wanda ya nuna turawa 81,474 ne suka mutu daga cutar.

An kara samun mutane 11 da suka kamu da cutar Coronavirus a jahar Legas, wanda hakan ya kawo adadin masu dauke da cutar a Najeriya zuwa 373, ta kashe 11 yayin da 99 suka warke.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel