An samu karin masu cutar Coronavirus 11 a Najeriya, jimilla 373
Cibiyar Takaita Yaduwar Cututtuka ta Najeriya, NCDC, a jiya ta tabbatar da sabbin mutane 3O da suka kamu da coronavirus a kasar wadda hakan ya kawo jimillar masu cutar a kasar zuwa 373.
Mutum 11 ne kuma cutar ya kashe a kasar a halin yanzu.
A cewar hukumar ta NCDC, "Kawo yanzu an tabbatar da masu cutar 373, 99 sun warke an sallame su yayin da mutane 11 sun mutu sakamakon cutar a Najeriya."
A baya, NCDC ta ruwaito cewa an samu karin mutane 19 da suka kamu da cutar a jihohi biyar
14 a Lagos
2 a Abuja
1 a Kano
1 a Akwa Ibom
1 a Edo
Daga bisani bayan karfe 11 na daren Talata ta sake ruwaito wa cewa, "an samu karin mutum 11 masu cutar a jihar Legas."
DUBA WANNAN: Shekau ya saki sabon sakon murya a kan maganin coronavirus
Sakon da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter ya ce,"
“A karfe 11:OO na daren 14 ga Afrilu, mutane 373 suka kamu da COVID19 a Najeriya. 99 sun warke, kuma 11 sun mutu.“
"A karfe 11 na daren 14 ga watan Afrilu, an samu bullar cutar #COVID19 a jihohi 19 da birnin tarayya."
Hukumar ta bayar da kididdigan masu cutar a jihohin Najeriya kamar haka
Legas - 214
Osun - 2O
Edo - 15
Oyo - 11
Ogun - 9
Bauchi - 6
Kaduna - 6
Akwa Ibom - 6
Katsina - 5
Kwara - 4
Kano - 4
Ondo - 3
Delta - 3
Enugu - 2
Ekiti - 2
Rivers - 2
Benue - 1
Niger - 1
Anambra - 1
Ta kara da cewa hukumar tana daukan matakan da suka dace domin dakile yaduwar cutar a kasar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng