Amala ba ya maganin coronavirus - Gwamnatin jihar Kwara

Amala ba ya maganin coronavirus - Gwamnatin jihar Kwara

Gwamnatin jihar Kwara ta karyata ikirarin da wasu ke yi a jihar na cewa abincin da ake amfani da doya wurin sarrafa shi wato Amala na maganin COVID-19.

Sakataren dindindin a maaikatar lafiya na jihar, Dr Abubakar Ayinla ya karyata jita-jitar a ranar Talata 14 ga watan Afrilu yayin taron kwamitin yaki da COVID-19 a jihar.

Ayinla ya ce gwamnatin jihar ta kafa kwamitin wayar da kan mutane domin dakile yaduwar labaran bogi a jihar a kan abubuwan da suka shafi kwayar cutar ta coronavirus.

Ya yi bayanin cewa an kafa kwamitocin ne domin dakile yaduwar karya da tsorata mutane inda ya sake tunatarwa cewa a halin yanzu babu maganin cutar kuma Amala bata maganin cutar.

Amala ba ya maganin coronavirus - Gwamnatin jihar Kwara
Amala ba ya maganin coronavirus - Gwamnatin jihar Kwara
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe mafarauta 11 a Katsina

Ayinla ya ce wadanda aka tabbatar suna dauke da cutar a jihar suna wurin killace mutane da ke Sobi inda ya kara da cewa suna samun sauki kuma gwamnatin jihar na kulawa da su.

Har wa yau, Direktan Hukumar Lafiya bai daya na jihar Dr Micheal Oguntoye ya yi bayanin cewa a halin yanzu akwai mutane uku masu dauke da COVID-19 a jihar.

A cewarsa, a halin yanzu akwai gadaje 3OO a asibitin killace masu cutar da ke Sobi da aka tanada a mataki daban daban ciki har da sashin wadanda cutar ta yi musu illa sosai.

Ya bayyana cewa asibitin na Sobi dungurungun an sauya shi zuwa asibitin killace masu dauke da kwayar cutar ta coronavirus.

Wasu wuraren da aka mayar zuwa asibitocin killace masu dauke da cutar sun hada da sansanin masu zuwa aikin hajji da kuma wani sansanin killacewa a Offa.

Hukumar kiyayye cututtuka masu yaduwa na Najeriya, NCDC, ta ce a halin yanzu akwai mutane hudu masu dauke da cutar a jihar ta Kwara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164