Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 19 yau a Najeriya, jimilla 362

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 19 yau a Najeriya, jimilla 362

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane sha tara (19) da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Talata, 14 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An samu karin mutane ashirin (20) sun kamu da #COVID19;

14 aLagos

2 a Abuja

1 a Kano

1 a Akwa Ibom

1 a Edo

“A karfe 9:20 na daren 14 ga Afrilu, mutane 362 suka kamu da COVID19 a Najeriya. 99 sun warke, kuma 11 sun mutu.“

“An tabbatar da bullar cutar a jihohi 19 a Najeriya.“

KU KARANTA: Iyalan mamaci 5 ko 6 kadai muka amince su yiwa gawa Sallar Jana'iza - Gwamnatin Saudiyya

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 19 yau a Najeriya, jimilla 362
Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 19 yau a Najeriya, jimilla 362
Asali: Facebook

Ga jerin jihohi:

Lagos- 203

FCT- 58

Osun- 20

Edo- 16

Oyo- 11

Ogun- 9

Bauchi- 6

Kaduna- 6

Akwa Ibom- 5

Katsina-5

Kwara- 4

Kano- 4

Ondo- 3

Delta- 3

Enugu- 2

Ekiti- 2

Rivers-2

Benue- 1

Niger- 1

Anambra- 1

A bangare guda, Ministan labarai, Lai Mohammed, ya ce gwamnatin tarayya ba zata iya raba wa yan Najeriya kudaden tallafi da hukumomi masu zaman kansu suka bayar don yakar cutar coronavirus ba.

A cewar NAN, ministan ya bayar da dalilan da yasa ba za a ba al’umman kasar kudin ba, a lokacin da ya bayyana a shirin “Politics Nationwide”, na Radio Nigeria a ranar Talata.

Ya yi martani ne ga wata bukata da ke naman a raba wa yan Najeriya wani bangare na kudaden domin su toshe gibin da dokar hana fita ya yi masu.

Ministan ya ce kudaden na inganta harkar lafiya ne, sannan cewa ba za a iya amfani dashi wajen samar da kayan rage radadi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel