Masu garkuwa da mutane sun sace matar basarake da yarsa

Masu garkuwa da mutane sun sace matar basarake da yarsa

- Masu garkuwa da mutane sun sace mata da diyar wani basarake a jihar Oyo

- Kamar yadda ganau suka bayyana, an sace sarauniyar da gimbiyar ne bayan sun dawo daga ziyara

- Majiyoyi da dama sun bayyana cewa ana zargin Fulani makiyaya ne da garkuwa da matan biyu

Anyi garkuwa da mata da diyar Oba Olusanjo Ojo, Baba-Aso na garin Igbole da ke Igboora, babban birnin karamar hukumar Ibarapa ta jihar Oyo.

Wakilin jaridar Leadership ya tabbatar da cewa, matar basaraken mai suna Olori Funbi Ojo da diyarsu da ta dawo daga kwalejin aikin noma na jihar anyi garkuwa dasu.

Idan zamu tuna, babu dadewa ne aka kashe wani mai likita mai suna Alhaji Yusuf Oko-Oloyun a Igboora, garin da ke da makwabtaka da Igbole.

Majiyoyi da dama sun ce ana zargin Fulani makiyaya ne da garkuwa da matan biyu a gonar Keji Abra da ke yankin Igbole na Igboora wajen karfe 8:15 na daren jiya.

Matukin motar wanda shima dan basaraken ne, yayi sa'ar tserewa daga wurin masu garkuwa da mutanen.

Masu garkuwa da mutane sun sace matar basarake da yarsa
Masu garkuwa da mutane sun sace matar basarake da yarsa
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Matar El-Rufa'i ta caccaki danta da yayi barazanar fyade

Duk da har yanzu ba a tuntubi 'yan uwan wadanda aka yi garkuwa dasu din ba, an gano cewa 'yan sa kai sun fara shiga daji don kokarin ceton wadanda aka sace.

Wata majiya wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce an sacesu ne a kusa da fadar.

Majiyar ta kara da cewa matar da 'yarta, wacce kwararriyar ma'aikaciyar jinya ce wacce ke hidimar kasa, suna dawowa ne daga wata ziyara a yayin da aka sacesu.

"An yi garkuwa da wasu a Igboora wajen karfe 8:15 na dare. Matar basarake ce da 'yarsu aka sace," majiyar tace.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Olugbenga Fadeyi ya ce jami'an 'yan sanda sun tsananta bincike tare da kokarin ceto wadanda aka yi garkuwa da su din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel