Yanzu-yanzu: An sake sallaman mutane 8 da suka warke daga cutar Coronavirus

Yanzu-yanzu: An sake sallaman mutane 8 da suka warke daga cutar Coronavirus

Gwamnatin jihar Legas ta ce ta sake sallamar masu cutar Coronavirus takwas da suka samu waraka a asibitin jinyar cututtuka dake unguwar Yaba ta jihar.

Gwamnatin jihar ta bayyana hakan ne ta shafin Tuwitan gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu a ranar Talata, 14 ga watan Afrilu.

Gwamnan yace: “Muna sake samun labarai masu dadi daga asibitin jinyar cututtukarmu dake Yaba.“

“An samu karin mutane takwas: mata biyu da maza shida da gwajinsu ya nuna cewa sun warke gaba daya daga cutar COVID19. Tuni an sallamesu kuma sun koma wajen iyalansu.“

“Hakan ya kawo adadin mara lafiya da mukayi jinya kuma muka sallama daga asibitocinmu zuwa 69.“

“Dan Alah mu cigaba da bin dukkan shawarin masana kiwon lafiya.“

A yanzu haka, jihar Legas ce jiha mafi yawan masu dauke da cutar inda mutane 192 cikin 343 na kasa gaba daya suke.

KU KARANTA FG ta fadi ranar da 'yan N-Power za su fara samun alat

Yanzu-yanzu: An sake sallaman mutane 8 da suka warke daga cutar Coronavirus

Yanzu-yanzu: An sake sallaman mutane 8 da suka warke daga cutar Coronavirus
Source: Twitter

Kawo yanzu, cutar Coronavirus ta kashe fiye da mutane 120,000 zuwa karfe 12 na ranar Talata, 14 ga watan Afrilun 2020.

Alkalumma sun bayyana tun daga watan Disamba da aka samu bullar cutar a China zuwa yau, ta kashe mutane 120,013 inda kashi 70 daga ciki duk yan kasashen Turai ne.

AFP ta ce ta tattara wadannan alkalumma ne daga bayanan da hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO, take fitarwa ne a kullum, wanda ya nuna turawa 81,474 ne suka mutu daga cutar.

A wani labari daban, Wani Kansila a karamar hukumar Katcha ta jihar Neja ya bace bat da kayan abinci da aka bashi ya rabawa mutanen yankinsa domin saukake radadin dokar zama a gida da gwamnati ta sanya.

Gwamnatin jihar ta sanya dokar ta baci ne domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a jihar.

An nemi Kansilan an rasa bayan bashi buhuhunan kayan hatsi 30 da aka bukaci ya rabawa mutane.

Sakataren gwamnatin jihar wanda shine shugaba kwamitin yakin COVID-19 a jihar, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya tabbatar da aukuwan haka kuma yace wannan abin takaici ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel