Yayi wuf! Kansilan da aka baiwa kayan abinci ya rabawa mutane ya bace bat

Yayi wuf! Kansilan da aka baiwa kayan abinci ya rabawa mutane ya bace bat

Wani Kansila a karamar hukumar Katcha ta jihar Neja ya bace bat da kayan abinci da aka bashi ya rabawa mutanen yankinsa domin saukake radadin dokar zama a gida da gwamnati ta sanya.

Gwamnatin jihar ta sanya dokar ta baci ne domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a jihar.

An nemi Kansilan an rasa bayan bashi buhuhunan kayan hatsi 30 da aka bukaci ya rabawa mutane.

The Nation ta tattaro cewa Kansilan na cikin kwamitin da aka nada domin rabawa mutane kayan masarufi a yankin.

Sakataren gwamnatin jihar wanda shine shugaba kwamitin yakin COVID-19 a jihar, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya tabbatar da aukuwan haka kuma yace wannan abin takaici ne.

Alhaji Ahmed Ibrahim ya nuna bacin ransa kan abinda Kansilan yayi inda yace yanzu al'ummarsa zasu sha wahala saboda halin ha'inci da rashin godiyan Allah na shugabansu.

A cewar, an baiwa kowani yankin mazabu 274 dake kananan hukumomi 25 na jihar buhun Shinkafa 10, Masara 10, da Gero 10 kuma an nada kwamitocin rabawa a kowace karamar hukuma.

“An nada kwamitoci a dukkan yankuna 274 dake jihar. Kwamitin ya hada da Kansila, Mhugaban jam“iyya, Maigari, da Malamin addini domin rabawa mutane kayan hatsin.“ SSG Ahmed yace

Ya ce jamian tsaro sun bazama neman Kansilan kuma zai fuskanci fushin hukumar idan aka kamashi.

Yayi wuf! Kansilan da aka baiwa kayan abinci ya rabawa mutane ya bace bat
Yayi wuf! Kansilan da aka baiwa kayan abinci ya rabawa
Asali: UGC

KU KARANTA Gwamnatin jihar Katsina a umurci ma'aikatanta su koma bakin aiki

A ranar 1 ga Afrilu, mun kawo muku rahoton cewa Wani direban motan haya da ya kamu da cutar Coronavirus ya gudu daga inda aka killaceshi a garin Bida, jihar Neja kuma na bazama nemansa yanzu.

Kwamishanan kiwon lafiyan jihar, Dakta Mohammed Makunsidi, ya alanta nemansa ruwa a jallo kuma gwamnati ta nada kwamiti na musamman domin nemoshi.

Yayinda yake jawabi ga manema labarai jiya a Minna, Makunsidi yace: "Mun yi mamakin guduwarsa kuma yadda ya gudu daga asibitin abin mamaki ne garemu har yanzu amma an harzuka wajen kamoshi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel