EU ta bawa Najeriya tallafin Yuro miliyan £50 don ta yaki annobar covid-19

EU ta bawa Najeriya tallafin Yuro miliyan £50 don ta yaki annobar covid-19

Kungiyar hadakar kasashen nahiyar Turai (EU) ta bawa Najeriya tallafin Yuro miliyan hamsin (£50m) domin yaki da annobar cutar covid-19.

Shugaban tawagar wakilan EU, Ambasada Ketil Karlsen, ne ya sanar da hakan yayin ziyarar da suka kai wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa ranar Talata.

Yayin ziyarar, tawagar wakilan ta mika sakon jinjinar EU ga shugaba Buhari a kan kokarin da gwamnatin Najeriya ta ke yi na yaki da annobar covid-19.

Da yake gabatar da jawabi, shugaba Buhari ya mika godiyarsa ga EU a kan tallafin kudin da ta bawa Najeriya domin yakar annobar cutar covid-19.

Yawan kudi ya kai biliyan N21 idan aka juya shi zuwa kudin Najeriya.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa kudaden za su matukar taimakawa kokarin Najeriya na ganin ta shawo kan annobar cutar covid-19 kafin ta karada cikin al'umma.

DUBA WANNAN: Dalilin da ya sa ba zamu iya rufe yankin arewa ba - Gwamnoni

"Kudin zai yi mana matukar amfani wajen sake bunkasa bangaren kiwon lafiya," a cewar Buhari.

Kazalika, ya mika sakon ta'aziyyar Najeriya ga EU a kan asarar rayukan da aka samu a nahiyar Turai sakamakon barkewar annobar covid-19.

"Mu na mika sakon ta'aziyya ga jama'ar nahiyar turai a kan barnar da annobar cutar covid-19 ta yi a nahiyar. Kamar yadda tarihi ya nuna, turai da sauran sassan duniya za su ga bayan wannan iftila'i," a cewar shugaba Buhari.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa ba zai manta gudunmawar da EU ta bawa Najeriya ba a irin wannan lokaci duk da irin kalubalen da yankin turai ke ciki sakamakon annobar cutar coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel