Da duminsa: An damke mai Coronavirus da ya gudu daga asibiti a Anambara

Da duminsa: An damke mai Coronavirus da ya gudu daga asibiti a Anambara

Kwamishanan kiwon lafiyan jihar Anambara, Dakta Vincent Okpala, a ranar Litinin ya bayyana cewa mutumin da ya kawo Coronavirus jihar kuma ya gudu daga baya ya shiga hannu.

Kwamishanan ya bayyanawa manema labarai a Awka cewa an damke mutumin cikin inda ya boye kuma abin da ban takaici.

Ya ce an killace akalla mutane 29 wanda ya hada da ma'aikata kiwon lafiya, yan 'uwansa, da abokan huldansa.

Okpala yace “Mun nemi mutumin daga karfe 8 na dare zuwa 3 na dare bayan cibiyar takaita yaduwar cututtuka suka tuntubi gwamnatin jihar cewa sakamakon gwajinsa ya fito kuma ya kamu da cutar.

“Tare da ni ake shiga wuraren da haka kawai ne ba zan shiga cikin dare ba, muna kwankwasa kofofin mutane muna tashinsu daga bacci domin nemansa.“

“Mutumin ya gudu daga asibiti kuma bai kamata yayi hakan ba.“

Yace abinda ya kamata ayi shine a killace mutumin “amma kawai ya arce kafin sakamakonsa ya fito, kuma yayinda na kira Likitan dake lura da shi, ya fada min cewa mutumin ba ya asibiti, sai muka fara nemansa.“

KU KARANTA Sojoji sun tare dumbin matafiya a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja

Da duminsa: An damke mai Coronavirus da ya gudu daga asibiti a Anambara

Da duminsa: An damke mai Coronavirus da ya gudu daga asibiti a Anambara
Source: Depositphotos

A karshen makon da ya gabata, mun kawo muku rahoton cewa an samu tashin hankali a jihar Anambara yayinda aka nemi mutumin farko da ya kamu da cutar Coronavirus a jihar aka rasa.

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar ranar Juma'a cewa an tabbatar da bullar cutar ta COVID-19 a jihar.

Tun lokacin, al'ummar jihar sun kidime bayan samun labarin cewa mutumin ya ziyarci asibitoci daban-daban uku a jihar.

Hakazalika ya yi mu'amala da mutane da dama kafin arcewa.

Amma kwamishanan kiwon lafiya na jihar Anambara, Dakta Vincent Okpala, da kwamishanan yada labarai, C Don Adinuba, sun ce mutane su kwantar da hankulansu.

Sakamakon haka, gwamnan jihar, Willie Obiano, ya sanar da cewa a kulle jihar gaba daya ba tare da bata lokaci ba, a cewar rahoton The Nation.

Dokar hana fitan za ta fara aiki ne ranar Litinin inda za a fara da dukkan tashohin mota.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel