Azumin bana babu Tafsiri a Masallacin Sultan Bello na Kaduna – Babban Limami

Azumin bana babu Tafsiri a Masallacin Sultan Bello na Kaduna – Babban Limami

Tun bayan bullar annobar nan mai toshe numfashi, watau Coronavirus, an samu sauye sauye da dama a al’amuran duniya gaba daya, wanda ya sauya salon tafiyar da hidindimu da yawa

A nan gida Najeriya ma wannan annoba ta kawo sanadiyyar sauya salon tafiya da al’amura, tun daga kulle makarantu, kulle kasuwanni, wuraren ibada da ma karya tattalin arziki.

KU KARANTA: Ka taimake mu da kudin tallafi da cibiyoyin gwajin Coronavirus – gwamnonin Arewa ga Buhari

Wannan tasa kwamitin Masallacin Sultan Bello dake garin Kaduna ta yanke shawarar dakatar da gudanar da tafsirin Al-Qur’ani mai girma kamar yadda aka saba yi a cikin Masallacin.

Fitaccen Malamin nan, Sheikh Ahmad Gumi ne yake gudanar da tafsiri a Masallacin a duk lokacin azumin watan Ramadana, amma an samu sauyi a azumin bana saboda COVID-19.

Babban limamin Masallacin, Farfesa Muhammad Sulaiman Adam ne ya bayyana haka, inda yace a bana Malam Ahmad Gumi zai gudanar da tafsirin ne daga wani wuri na daban.

Sulaiman yace Malam Gumi ne kadai zai gudanar da Tafsirin tare da majabakinsa, kuma za’a watsa karatun a kafafen sadarwa na gani da na saurare, da shafukan sadarwar zamani.

Haka zalika, Sheikh Sulaiman ya kara da cewa Masallacin Sultan Bello zai cigaba da zama a garkame har sai lokacin da gwamnati ta bayar da izinin bude Masallatai.

Daga karshe Shehin Malamin ya bayyana dalilin daukan wannan mataki shi ne don dakile yaduwar cutar, don haka ya nemi Musulmai su cigaba da addu’a domin Allah Ya yaye masifar.

Shi ma Sheikh Gumi ya tabbatar da bayanin Sheikh Sulaiman, inda yace zai gudanar da tafisirin bana ne a wani wuri da ya dace da ka’idojin da hukuma ta shimfida da na masu kiwon lafiya.

A wani labarin kuma, Kungiyar gwamnonin Arewa ta nemi shugaban kasa Buhari ya agaza musu da kayan tallafi don raba ma jama’a da kuma cibiyoyin gwajin cutar Coronavirus.

Shugaban kungiyar, Gwamna Simon Lalong ne ya yi rokon a ranar Litinin bayan kammala taron gwamnonin da suka yi ta yanar gizo, inda yace da haka ne zasu iya yaki da cutar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel