Kaico! Jirgin yakin Najeriya ya yi ma kananan yara luguden wuta a jahar Borno

Kaico! Jirgin yakin Najeriya ya yi ma kananan yara luguden wuta a jahar Borno

Akalla mutane 17 ne suka mutu yayin da jirgin yakin Najeriya ya jefa bamabamai a kauyen Sakotoku dake karamar hukumar Dambo ta jahar Borno, bisa kuskure.

Jaridar TheCable ta ruwaito wadanda suka mutu a wannan harin sune mata da kuma kananan yara, wanda suke wasa da zaman shan iska a karkashin wata bishiyar mangwaro.

KU KARANTA: Buhari ya ce babu shiga babu fita a Legas da Abuja, amma zasu cigaba da raba kudade

Majiyoyi daga gidan Soja sun bayyana an jefa bamabaman ne bayan rundunar Sojan sama ta samu labarin taruwar yan Boko Haram a kauyen, don haka ta shirya musu luguden wuta.

Inda ya kamata a kai harin shi ne wani yanki a Korongilum dake makwabtaka da Sakotoku da kimanin nisan kilomita 12, a nan ne mayakan Boko Haram din suka taru.

Kaico! Jirgin yakin Najeriya ya yi ma kananan yara luguden wuta a jahar Borno
Kaico! Jirgin yakin Najeriya ya yi ma kananan yara luguden wuta a jahar Borno
Asali: UGC

“Bamu sani ba ko an samu gibi a musayar bayani ne tsakanin Sojojin sama da na kasa a lokacin da jiragen rundunar Sojin sama suka jefa bamabamai a kauyen ba, mutane 17 sun mutu, yawancinsu mata da kananan yara ne dake wasa a kasar bishiyar mangwaro.

“Da dama kuma sun samu rauni, kuma an garzaya dasu zuwa asibitin runduna ta 25 dake Damboa, wadanda ke cikin mawuyacin hali kuma an mika su zuwa Maiduguri. Wadanda harin ya shafi gidajensu kuma sun zarce Damboa.” Inji majiyar.

A wani labari kuma, mutane 7 sun mutu a ranar 12 ga watan Afrilu yayin da yan ta’addan Boko Haram suka kai hari kwantan bauna a kan wasu motocin haya guda 2 a jahar Borno.

Premium Times ta ruwaito Boko Haram ta tare motocin ne a wajen garin Auno, kimanin kilomita 20 daga garin Maiduguri, a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Wani matafiyi da ya yi ido hudu da gawarwakin ya bayyana cewa ya kirga gawarwaki guda 7 a wajen garin Auno, kuma an fada musu a daren jiya aka kai harin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel